Ku bamu mako daya domin ganin yiwuwar rage farashin mai, gwamnatin tarayya ga kwadago

Ku bamu mako daya domin ganin yiwuwar rage farashin mai, gwamnatin tarayya ga kwadago

- Kungiyar NLC ta bukaci gwamnati ta cire karin da tayi kan fetur zuwan N170

- Gwamnati ta ce ba ita ta kara farashin mai fa, kawai ta cire hannunta daga lamarin

Gwamnatin tarayya ta bukaci mako daya kacal wajen kungiyar kwadago NLC domin duba yiwuwar janye karin farashin da akayiwa man fetur a watan Nuwamba.

Shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya bayyana wannan bukatar ne a ganawarsu na ranan Alhamis a fadar shugaban kasa, rahoton The Nation.

Kyari ya bayyanawa NLC cewa kamfanin NNPC kadai ba zai iya janye farashin man ba ba tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki ba.

Kungiyar NLC ta amince da hakan kuma an dage zaman zuwa ranar 7 ga Disamba, 2020.

Kungiyar kwadagon ta bukaci gwamnati ta janye wannan sabob kari na farashin mai da tayi saboda hakan ya sabawa yarjejejiyar da akayi a Satumba.

A karshen zaman da aka kwashe sa'o'i 3 anayi, Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyanawa manema labarai cewa kwamitin za ta bayyanawa Buhari matsayar NLC tunda shine Ministan Man Fetur.

"Nan da ranar Litinin, 7 Disamba, zamu dawo, saboda sakon da yan kwadago suka zo dashi daya ne. Suna son a janye sabon karin zuwa inda yake. Saboda haka zamu kai wannan sako wajen shugabanninmu," Ngige yace.

Mataimakin shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero ya ce yana kyautata zaton cewa udan aka dawo ranar 7 ga Disamba, za'a janye karin.

KU KARANTA: Wannan rashin tausayi ne - IPMAN ta yi Alla-wadai da karin farashin mai zuwa N170

Ku bamu mako daya domin ganin yiwuwar rage farashin mai, gwamnatin tarayya ga kwadago
Ku bamu mako daya domin ganin yiwuwar rage farashin mai, gwamnatin tarayya ga kwadago
Asali: Twitter

DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN

Mun kawo muku cewa Farashin man yanzu ya tashi zuwa N170 da lita a gidajen mai.

A takardar da kamfanin ta saki ranar 11 ga Nuwamba, an gano cewa za'a fara sayar da mai a wannan farashin ranar 13 ga Nuwamba, 2020.

Bayan haka, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa har yanzu ba'a gama cire tallafi kan kayayyakin man fetur ba a kasar.

Haka Ministan Man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana a hirar da yayi ranar Litinin da Seun Okinbaloye na Channels TV.

A cewarsa, wannan kawai somin tabi ne, yanzu aka fara cire tallafi kan kayan man fetur. "Yanzu fa kawai muna kokarin tare abu ne kada ya balle. Bamu fara ainihin cire tallafin mai gaba daya ba ta bangaren kasuwar canji," Sylva yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel