Yanzu-yanzu: ASUU sun amince zasu janye yajin aiki, an kara musu N5bn

Yanzu-yanzu: ASUU sun amince zasu janye yajin aiki, an kara musu N5bn

- Bayan awanni 10 ana tattaunawa, da yiwuwa dalibai zasu koma makaranta ranar Litinin

- Gwamnati ta karawa malaman jami'an naira bilyan biyan kan tayin da ta musu a baya

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU ta amince za ta janye yajin aikin da aka kwashe watanni takwas anayi kuma hakan ya dakatad da karantun dalibai a jami'o'in gwamnati.

Kungiyar ta amince da da janye yajin aikin ne a ganawarta da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ministan kwadago, Chris Ngige, a Abuja ranar Juma'a, The Punch ta ruwaito.

Bayan haka, gwamnati ta yi alkawarin biyan ASUU kudi N70bn, sabanin N65bn da tayi musu tayi.

Yanzu-yanzu: ASUU sun amince zasu janye yajin aiki, an karawa musu N10bn
Yanzu-yanzu: ASUU sun amince zasu janye yajin aiki, an karawa musu N10bn Hoto: Tambari
Asali: Twitter

KU KARANTA: PDP: Kotu ta dakatar da aikin shugabannin rikon kwarya a Jihar Ebonyi

Mun kawo muku cewa Gwamnatin tarayya a ranar Juma'a ta cigaba da tattaunawa da kungiyar malaman jami'o'inNajeriya ASUU domin kawo karshen yajin aiki wata takwas dake gudana.

Ganawar ranar Juma'a, da aka shirya farawa karfe 11 na safe bai yiwu ba sai misalin karfe 2:25 ba sallar Juma'a kuma Ministan Kwadago, Chris Ngige, ke jagorantan zaman.

Ya ce gwamnati ta yiwa kungiyar tayin wasu abubuwa makon da ya gabata kuma "sun yi alkawarin tattaunawa da mambobinsu kafin suk dawo mana da amsa."

Gabanin haka, gwamnatin tarayya ta amince da bukatun kungiyar malaman jami'a ASUU cewa a togaciye mambobinta daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

A zaman da gwamnatin tayi da shugabannin ASUU ranar Juma'ar da ta gabata, ta hakura kan wasu lamura wanda ya hada da wajabta biyan malaman ta IPPIS da kuma kar musu kudin alawus da kudin gyaran jami'o'i.

DUBA NAN: Matawalle ya jinjina yiwuwar barin PDP, ya ce 'Ina fuskantar matsaloli; na yi wa Umahi murna'

Yayin karanto abubuwan da suka tattauna bayan sa'o'i bakwai ana tattaunawa a dakin taron ma'aikatar kwadago, Ministan, Chris Ngige, ya ce gwamnati ta amince a biya mambobin ASUU albashinsu tun daga watan Febrairu zuwa Yuni da tsohon manhajar GIFMIS.

Hakazalika gwamnatin ta amince da kara kudin alawus na malaman daga N30bn zuwa N35bn, sannan kudin gyaran jami'o'i daga N20bn zuwa N25bn.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

https://youtu.be/FWA_8Q5Zowk

Asali: Legit.ng

Online view pixel