Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta saduda, ta amince a cire ASUU daga IPPIS, ta bada N65bn kudin alawus

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta saduda, ta amince a cire ASUU daga IPPIS, ta bada N65bn kudin alawus

- Daliban jami'a su fara shirye-shiryen komawa makaranta, da yiwuwa yajin aiki ya zo karshe

- Gwamnatin tarayya ta janye daga matsayarta na tilastawa malaman jami'a amfani da manhajar IPPIS

- Bayan haka an yiwa malaman jami'a karin bilyan 10 kan tayin da aka yi musu a baya

Bayan watanni 8 ana muhawara, gwamnatin tarayya ta amince da bukatun kungiyar malaman jami'a ASUU cewa a togaciye mambobinta daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

A zaman da gwamnatin tayi da shugabannin ASUU ranar Juma'a, ta hakura kan wasu lamura wanda ya hada da wajabta biyan malaman ta IPPIS da kuma kar musu kudin alawus da kudin gyaran jami'o'i.

Yayin karanto abubuwan da suka tattauna bayan sa'o'i bakwai ana tattaunawa a dakin taron ma'aikatar kwadago, Ministan, Chris Ngige, ya ce gwamnati ta amince a biya mambobin ASUU albashinsu tun daga watan Febrairu zuwa Yuni da tsohon manhajar GIFMIS.

Hakazalika gwamnatin ta amince da kara kudin alawus na malaman daga N30bn zuwa N35bn, sannan kudin gyaran jami'o'i daga N20bn zuwa N25bn.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin zaben sarki, Wazirin Zazzau

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta saduda, ta amince a cire ASUU daga IPPIS, ta bada N65bn kudin alawus
Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta saduda, ta amince a cire ASUU daga IPPIS, ta bada N65bn kudin alawus Channels TV
Asali: Twitter

Wannan sanarwa ya biyo bayan shirin da gwamnatin tarayya keyi na yiwa kungiyar ASUU kishiya.

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta shiga yajin-aiki a Najeriya tun watan Maris, 2020.

Ministan kwadago da samar da aikin-yi na kasa, Chris Ngige, ya kyankyasa wa mutnae wannan a lokacin da ya gana da kungiyar CONUA a Abuja.

KU KARANTA: Kakakin majalisar wakilai ya tona asirin dan sandan da ya bindige mai jarida a Abuja

A ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, 2020, Dr, Niyi Sunmonu ya jagoranci kungiyarsa ta CONUA, su ka zauna da Ministan a birnin tarayya.

Kungiyar CONUA ta na kunshe ne da malaman jami’o’in da su ke adawa da tafiyar ASUU. Gwamnati ta nuna za ta yi wa wannan kungiya rajista.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel