PDP: Kotu ta dakatar da aikin shugabannin rikon kwarya a Jihar Ebonyi

PDP: Kotu ta dakatar da aikin shugabannin rikon kwarya a Jihar Ebonyi

- An shigar da karar Shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi a kotu

- Shugabannin da aka ruguza suna kalubalantar matakin da aka dauka

- Alkali ya yi na’am da rokon da Lauyan dake karar NWC-PDP ya shigar

Babban kotun jihar Ebonyi da ke zama a Abakaliki, ya dakatar da shugabannin PDP na rikon-kwarya da aka kafa daga gabatar da kansu da sunan jam’iyya.

A ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, 2020, Alkali ya ce shugabannin rikon-kwayar su dakata daga shiga ofis bayan ‘yan taware sun shigar da kara gaban kotu.

Bangaren Onyekachi Nwebonyi da majalisarsa suna karar matakin da uwar jam’iyya ta dauka na sauke su daga mukaminsu bayan Dave Umahi ya sauya-sheka.

KU KARANTA: Ba na nadamar komawa jam'iyyar APC - Dave Umahi

Punch ta fitar da rahoto cewa an ruguza majalisar gudanar wa ta jam’iyyar PDP daga Abuja a sakamakon barin gwamnan jihar da aka yi ya tsere daga jam’iyya.

Uwar jam’iyya ta zabi mutane tara a karkashin Fred Ụdogu su rike shugabancin PDP a jihar Ebonyi a madadin Onyekachi Nwebonyi har zuwa lokacin da za ayi zabe.

Wannan ya sa Onyekachi Nwebonyi ya kai jam’iyya da shugabanninta kotu; Tsohon shugaban jam’iyyar ya na karar uwar jam’iyya da kuma Prince Uche Secondus.

Sauran wadanda ake tuhuma a gaban Alkali sune duka ‘yan majalisar SWC ta Fred Ụdogu.

KU KARANTA: Umahi zai sha kunya a hannun APC - PDP

PDP: Kotu ta dakatar da aikin shugabannin rikon kwarya a Jihar Ebonyi
Buhari da Gwamnan Jihar Ebonyi Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Lauyan tsohon shugaban na PDP, Roy Umahi ya fada wa Alkali an zalunci Ụdogu, a cewarsa ba ayi wa shugabannin jam’iyyar adalci wajen saukesu daga kujerunsu ba.

Umahi ya roki kotu ta dakatar da nadin shugabannin rikon kwarya da za ayi a jiha da kananan hukumomi da mazabu domin NWC ba ta da ikon ruguza shugabanni.

Alkali Elvis Ngele ya amince da duk bukatun da Lauyan ya gabatar, ya dage shari’ar zuwa Disamba.

A baya kun ji cewa Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya sake rabuwa da wasu hadimansa bayan komawar sa jam'iyyar APC daga PDP.

Gwamnan ya shahara da sallaman hadimansa, musamman bayan barinsa jam'iyyar PDP.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel