Kada a bude boda, zamu wahala, kungiyar manoma ga shugaba Buhari
- Ministar Kudi ta ce sun baiwa shugaba Buhari shawara ya bude iyakokin Najeriya
- An rufe iyakokin ne tun watan Agustam 2019 don hana shigo da kayayyaki
- Manoman Najeriya sun nuna mabanbancin ra'ayi kan shirin sake bude iyakokin
Manoman Najeriya a ranar Laraba sun yi Alla-wadai da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na sake bude iyakokin Najeriya na kasa.
Sun bayyana cewa bude iyakokin a yanzu da kayan abinci ke hauhawa abune mai hadarin gaskiya.
Sun ce kasashe makwabta da suka dogara kan Najeriya wajen samun kayan abinci zasu shigo kasar kuma hakan zai sa kayan abinci ya sake hauhawa, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar manoman Najeriya (AFAN) Arch. Kabiru Ibrahim, ya bayyanawa DT a hirar wayar tarho cewa bude bodan zai saukaka fitar da kayan abinci daga Najeriya zuwa kasashe masu makwabtaka da mu.
"Kuna ganin yanzu ana noma ana girba amma duk da haka kayan abinci na hauhawa saboda wasu dalilai,... inaga idan aka bude iyakokin, abin da hadari, " yace.
Manoman sun kara da cewa a tuna har yanzu akwai annobar cutar Korona kuma bari mutanen daga wajen sun shigowa Najeriya na iya kara harzuka kamuwar cutar a nan.
KU DUBA: Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi
Mun kawo muku cewa gwamnatin tarayya a ranar Talata ta bayyana cewa da yiwuwan a sake bude iyakokin Najeriya da aka rufe watan Agustan bara, Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana.
Ministar ta laburta a taron tattalin arzikin Najeriya da akayi a Legas cewa kwamitin da shugaba Buhari ya nada don duba ribar rufe iyakokin sun bashi shawaran cewa ya bude, The Sun ta ruwaito.
Saboda haka, tana kyautata zaton cewa Buhari zai dauki shawarar kuma ya aiwatar nan ba da dadewa ba.
Duk da cewa bata bayyana takamammen ranan da za'a bude ba, amma ko shakka babu tace za'a bude nan ba da dadewa ba.
KU KARANTA: Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng