Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi

Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi

- Bayan watanni biyu a rashinsa, hukumar Sojin Najeriya ta karrama Jarumi Kanal Bako

- Kanal Bako ya rasa rayuwarsa ne a faggen fama a Arewa maso gabas

- Gwamnan jihar Borno ya yi alhinin mutuwar Kana; Bako kuma yi yiwa iyalansa alkawari

Hukumar Sojin Najeriya ta amince da karawa Marigayi Kanal Dahiru Bako matsayi zuwa Birgediya Janar domin karramashi bisa sadakarwan da yayi, Murtala Abdullahi na jaridar HumAngle ya ruwaito.

Janar Bako ya rasa rayuwarsa sakamakon yaki da Boko Haram kuma an sanar da mutuwarsa bayan aikin da akayi masa a asbiti a Satumba.

Kungiyar ISWAP, wata ballin Boko Haram ce ta kai wannan hari.

Kanal Bako wanda ya kasance Birgade Kwamandan na 25 Task Force ya na zaman aikinsa a karamar hukumar Damboa, kilomita 85 zuwa Maiduguri, birnin jihar Borno.

Ya kasance Soja da ake matukar girmamawa bisa jaruntarsa da jagorantan Sojoji zuwa faggen dama har da daji mai hadari, Algarno.

"Ya yi yaki sosai. Ya kawar da makiya zaman lafiya kuma ya kare rayukan mutan jihar Borno har sai da ya sadaukar da rayuwarsa yana karesu" cewar gwamnan jihar Borno, Babagana zulum.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi

Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi
Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi Hoto: GovBorno
Source: Facebook

KU DUBA: Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya cika alkawarinsa na kyautan naira milyan ashirin da ya yiwa iyalan jarumin kwamandan da aka kashe a filin yaki da yan ta'addan Boko Haram.

Gwamnan ya sanar da hakan da safiyar Laraba, a shafinsa na Tuwita da Facebook.

A ranar Litinin ne rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Bayan Kanar Dahiru Chiroma Bako da aka kashe, Zulum ya sanar da baiwa iyalan sauran Sojoji uku da aka kashe tare da shi milyan biyu-biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel