Nan ba da dadewa ba zamu bude boda: Ministar Kudi, Zainab Shamsuna

Nan ba da dadewa ba zamu bude boda: Ministar Kudi, Zainab Shamsuna

- Bayan shekara daya da hana shigo da kayayyaki ta iyakokin Najeriya, da alamun an kusa budewa

- Farashin kayan abinci musamman shinkafa ya yi tashin gwauron zabo cikin shekara daya

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta bayyana cewa da yiwuwan a sake bude iyakokin Najeriya da aka rufe watan Agustan bara, Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana.

Ministar ta laburta a taron tattalin arzikin Najeriya da akayi a Legas cewa kwamitin da shugaba Buhari ya nada don duba ribar rufe iyakokin sun bashi shawaran cewa ya bude, The Sun ta ruwaito.

Saboda haka, tana kyautata zaton cewa Buhari zai dauki shawarar kuma ya aiwatar nan ba da dadewa ba.

Duk da cewa bata bayyana takamammen ranan da za'a bude ba, amma ko shakka babu tace za'a bude nan ba da dadewa ba

"Mun duba lamuran. Shugaban kasa ya kafa kwamiti kuma dukkan mambobin kwamitin suna masu bada shawaran ya kamata lokacin bude boda yayi."

"Saboda haka muna sa ran a bude iyakokin nan ba da dadewa ba. Shugaban kasa zai sanar da ranan," Tace.

KU KARANTA: Iyalan mai jaridan da dogarin Kakakin majalisa ya harbe sun bukaci N500m kudin diyya

Nan ba da dadewa ba zamu bude boda: Ministar Kudi, Zainab Shamsuna
Nan ba da dadewa ba zamu bude boda: Ministar Kudi, Zainab Shamsuna
Asali: Getty Images

Najeriya ta rufe iyakokinta na kasa a Agustan 2019 saboda shigo da makamai, muggan kwayoyi, da kayan masarufi Najeriya daga kasashen dake makwabta.

An rufe iyakokin ne domin karawa manoman shinkafar gida gwiwa domin tabbatar da Najeriya za ta iya ciyar da kanta.

A bangare guda, a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2020, Ministan ayyuka da gidajen Najeriya, Babatunde Raji Fashola, ya yi magana game da siyasar 2023 a gidan APC.

Babatunde Raji Fashola SAN ya ce yadda tsarin kama-kama ya yi aiki a zaben 2015, ya kamata idan an zo 2023, a bar mulki ya koma wa yan yankin kudu.

Jaridar Daily Trust ta ce tsohon gwamnan ya yi wannan magana ne a lokacin da wasu ‘ya ‘yan APC suke kokarin ganin an bar Arewa su cigaba da mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel