Buhari na buƙatar goyon baya don magance sheɗanun da ke Najeriya, in ji Tambuwal

Buhari na buƙatar goyon baya don magance sheɗanun da ke Najeriya, in ji Tambuwal

- Akwai wasu sheɗanu a Najeriya a cewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

- Gwamnan Sokoton ya ce Shugaba Buhari na buƙatar goyon baya don daƙile shaiɗanun

- A cewar gwamnan, sheɗanun ba su da wata buri sai kawo ruɗani a Najeriya

A yayin da Najeriya ke fama da rigingimunta, an yi kira da ƴan kasa su taru su mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ne ya yi wannan kirar kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Buhari na buƙatar goyon baya don magance sheɗanun da ke Najeriya, in ji Tambuwal
Buhari na buƙatar goyon baya don magance sheɗanun da ke Najeriya, in ji Tambuwal. Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

A cewarsa, dole a taimaka wa shugaban kasar kafin ya iya cin galaba kan sheɗanun da ke ƙasar.

Ya yi wannan jawabin ne a yayin da ya ke karɓar Shehun Bama a yayin da ya kai masa ziyarar ban girma.

Ya ce:

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ɗaliban ABU Zaria 17 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

"Ya zama dole muyi aiki tare a matsayin mu na al'umma da shugabanni mu goyi bayan gwamnatin tarayya don samar da zaman lafiya a sassar ƙasar.

"Za mu cigaba da taimakawa Shugaban ƙasa domin daƙile sheɗanun da ke fafutikan kawo tashin hankali a ƙasar mu."

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 8 ga watan Oktoban 2020 ya ce tattalin arzikin Najeriya na fuskantar matsaloli.

Shugaban na Najeriya ya ce akwai yiwuwar kasar ta sake fada wa cikin matsin tattalin arziki a watanni uku na karshen shekarar 2020.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel