Gwamnatin Kogi ta sanya haraji kan kowane burodi a jihar

Gwamnatin Kogi ta sanya haraji kan kowane burodi a jihar

- Gwamnatin Jihar Kogi ta bullo da sabon haraji da masu burodi za su rika biya wa kowanne burodi a jihar

- Kungiyar masu gasa burodin ta ce bata goyon bayan harajin don kowa na cikin mawuyacin hali sakamakon Covid 19

- Kungiyar ta ce zata tuntubi wanda aka dora wa alhakin karbar harajin daga hannun 'ya'yanta don samun karin bayani

Gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Amma, kungiyar masu gasa burodi reshen jihar sun bayyana cewa basu goyon harajin.

Wani jigo a kungiyar wanda aka sani da Godfirst ya ce suna shirye shiryen yadda zasu zauna da masu alhakin karbar kudin.

Gwamnatin Kogi ta sanya haraji ga kowane gasasshen Biredi
Gwamnatin Kogi ta sanya haraji ga kowane gasasshen Burodi. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

Godfirst ya ce sun karbi sanarwa daga ma'aikatar cewa an saka haraji "akan kowane burodi" da aka sarrafa.

"Takardar ta zo mana akan cewa an bada alhakin tattara kudade daga gidajen burodi zuwa gwamnatin jiha, don samar da haraji ga gwamnatin jihar", a cewarsa.

"Muna kokarin haduwa da masu alhakin tattara kudin amma har yanzu bamu samu damar haduwa dasu ba. Muna so mu gansu don ya yi mana karin bayani."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Ya ce masu gidajen burodi na shan wahala sakamakon tsadar rayuwa da annobar Korona ta haifar saboda haka baza su iya cika wannan umarni ba.

"Bamu ji dadin hakan ba, yanzu ba ciniki. Muna fuskantar kalubale, yanzu idan suka ce sai mun sake biyan wani kudi bamu san yadda zamu yi ba," a fadar sa.

Har yanzu an gaza jin ta bakin kwamishinan watsa labaran jihar Kinsley Fanwo dangane da lamarin.

A wasu ƴan bindiga sun sace hakimin garin Matseri na da ke ƙaramar hukumar Anka a Zamfara, Alhaji Halilu Matseri da yaransa huɗu.

Sun kuma kashe wani Maigaiya Matseri da ya yi ƙoƙarin ceto hakimin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel