Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

- 'Yan Jam'iyyar APP reshen Jihar Ebonyi sun fice zuwa jam'iyyar PDP tare da shugabannin su baki daya

- Tsohon shugaban APP ya ce sun dauki matakin ne ganin cewa jam'iyyar PDP ita kadai ce jam'iyya mai tausayin talaka

- Gwamnatin APC ta watsawa talaka kasa a ido ganin yadda ta kasa gudanar da mulki yadda ya dace

'Yan jam'iyyar Action Peoples Party, APP, da ba zasu gaza 20,000 ba, ciki har da manyan shugabannin jam'iyyar sun koma jam'iyyar PDP a jihar Ebonyi ranar Talata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Da yake shaidawa manema labarai a Abakaliki, tsohon shugaban jam'iyyar APP, Engr. Joshua Chinedum Elekwachi ya bayyana cewa dalilin da yasa suka yanke wannan shawara shine, sun tabbatar cewa "jam'iyyar PDP ita kadai ce jam'iyyar da ke kula da bukatar talaka, ba a iya Ebonyi ba har da kasa baki daya."

Yan jam'iyyar APP 20,000 sun koma PDP a Ebonyi
Yan jam'iyyar APP 20,000 sun koma PDP a Ebonyi. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

A cewar sa, "na dawo jam'iyyar PDP ne don hada kai da kuma aiki da mutanen kirkin Ebonyi don kwato jihar mu daga hannun yan siyasa masu azurta kansu, wanda suka lalata shugabanci kuma suka durkusar da jihar tsawon shekaru."

DUBA WANNAN: Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

Tsohon shugaban kungiyar shugabannin APP na kasa a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja, ya soki yadda gwamnatin tarayya karkashin jam'iyyar APC ke gudanar da tafiyar hawainiya a mulkin ta.

Ya ce gwamnatin APC ta watsawa talakawa kasa a ido ganin yadda suka kasa shawo kan matsalar tattalin arziki.

Ya ce: "zan koma jam'iyyar PDP tare da duk manyan shugabannin jam'iyyar APP a matakin jiha da kananan hukumomi tare da yan jam'iyyar fiye da 20,000 a fadin jihar.

"Saboda haka, yau, Talata, 17 ga Nuwamba 2020, gaba daya reshen jam'iyyar APP a nan jihar Ebonyi mun koma jam'iyyar PDP.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ɗaliban ABU Zaria 17 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

"A shekara biyar da ta gabata, abubuwa da dama sun faru wanda ya janyo da yawa daga cikin al'ummar Ebonyi suka ji rashin dadi, an watsar da su an kuma banzatar, amma lokaci ya yi da ubangiji zai dubi bayinsa ya kuma basu sabuwar gwamnati."

A wani labarin, bala'i ya afku a Jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel