Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce

Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce

- Wasu hotunan tagwaye mata da maza za su angwance ya karade kafafen sada zumuntar zamani

- Karamar yadda Legit.ng ta gano, an yi hotunan ne a cikin shirye-shiryen bikin tagwayen

- Tabbas amaren da angunansu sun matukar kayatar da jama'a inda aka dinga kwarara musu fatan alheri

Wasu hotunan tagwaye maza za su angwance da tagwaye mata sun bazu a kafafen sada zumuntar zamani.

A hotunan da suka karade kafafen sada zumuntar, an ga kyawawan samari wadanda tagwaye ne tare da kyawawan 'yan mata tagwaye.

Wannan lamarin ya matukar kayatar da jama'a inda suka dinga musu fatan alheri tare da kwararo musu addu'a.

Kamar yadda Legit.ng ta ga wani shafi mai suna northern hibiscuss a Instagram ya wallafa hotunan, an dinga musu fatan zaman lafiya da zuri'a tagari.

Ga dai kyawawan hotunan, mai karatu ya kashe kwarkwatar idanuwansa:

Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce
Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce. Hoto daga northern_hibiscuss
Asali: Instagram

KU KARANTA: Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa

Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce
Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce. Hoto daga northern_hibiscuss
Asali: Instagram

Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce
Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce. Hoto daga northern_hibiscuss
Asali: Instagram

KU KARANTA: Obasanjo zai nufi kasar Ethiopia domin aiwatar da wani babban al'amari

Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce
Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce. Hoto daga northern_hibiscuss
Asali: Instagram

Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce
Kyawawan hotunan tagwaye maza za su aura tagwàye sun janyo cece-kuce. Hoto daga northern_hibiscuss
Asali: Instagram

A wani labari na daban, an tirsasa wa wata yarinya mai shekaru 13 ta auri wani mutum mai shekaru 48, sannan ta kula da yaransa wadanda tsararrakinta ne, shafin Linda Ikei ya wallafa.

A cewar Abdulrazak, wani manomi, a cewarsa idan yana gona, amaryarsa tana iya ayyukan gida kuma za ta kula masa da yaransa, wadanda ya haifa da wasu matan da ya taba aura kafin ya aureta.

Bai dade da gina gidansa ba, inda yace a nan ne za su zauna tare da yaransa da ya haifa da wasu matan.

A cewarsa, "Ina matukar farin cikin samunta a matsayin mata, ina so in karasa rayuwata tare da ita, ta dinga kula min da yara.

"Zan cigaba da biya mata kudin makaranta kafin ta fara haifa min yara."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel