Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa

Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa

- Rundunar sojin sama ta OPERATION LAFIYA DOLE, ta ragargaji 'yan boko Haram a dajin Sambisa

- Al'amarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Nuwamba, wanda sojin suka kai hari wuraren Gobara da Sambisa

- Kakakin hukumar rundunar soji, Janar John Enenche ne ya sanar da hakan a matsayin wata nasarar

Rundunar sojin sama ta Operation LAFIYA DOLE, ta ragargaji 'yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar Borno, jaridar Leadership ta wallafa.

Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya ce rundunar ta yi harbin ne ta sama, a bangarori 2, bangaren Sambisa da Gobara, inda yace sun yi amfani da salo na musamman don kai wa 'yan Boko Haram din hari.

Ya ce sojojin sun yi harbin ne daidai wuraren da suke zargi. Saboda sai da suka duba kuma suka yi nazari a wuraren da 'yan ta'addan suka kafa daba, tukunna suka yi harbin. Hakan ya yi sanadiyyar kashe yawancinsu.

KU KARANTA: Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna

Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa
Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza sansanin 'yan Boko Haram a Sambisa. Hoto daga @Leadership
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ndume: Buhari na zagaye da manyan barayi a mulkinsa

A wani labari na daban, a kalla mutane 11 'yan bindiga suka kashe a sabon harin da su ka kai kauyen Albasu a Sabon Birni, karkashin karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna, Channels TV ta wallafa.

'Yan bindigan sun je ne da yawansu, inda suka afka wa kauyen da misalin karfe 1 na ranar Litinin. Sun bude wa mazauna kauyen wuta ta ko ina, sanadiyyar haka suka yi ajalin mutane da dama, sun kwashe shanaye da dabbobi masu yawa na kauyen.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Sunday Aruwan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an bi bayan 'yan ta'addan da nufin kama su.

Ya kuma bayyana yadda aka yi garkuwa da wasu mutane 2, sannan aka kashe 1 a Maraban Kajuru da ke karamar hukumar Kajuru a ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel