Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48

Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48

- Wani lokacin, auren dole yana zama rikici, wani lokaci kuma ya dore

- Wani mutum mai suna Abdulrazak mai shekaru 48 ya auri yarinya 'yar shekara 13

- A cewar manomin, idan ya tafi noma, ya san za ta iya kula masa da yara da gidansa

An tirsasa wa wata yarinya mai shekaru 13 ta auri wani mutum mai shekaru 48, sannan ta kula da yaransa wadanda tsararrakinta ne, shafin Linda Ikei ya wallafa.

A cewar Abdulrazak, wani manomi, a cewarsa idan yana gona, amaryarsa tana iya ayyukan gida kuma za ta kula masa da yaransa, wadanda ya haifa da wasu matan da ya taba aura kafin ya aureta.

Bai dade da gina gidansa ba, inda yace a nan ne za su zauna tare da yaransa da ya haifa da wasu matan.

A cewarsa, "Ina matukar farin cikin samunta a matsayin mata, ina so in karasa rayuwata tare da ita, ta dinga kula min da yara.

"Zan cigaba da biya mata kudin makaranta kafin ta fara haifa min yara."

Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48
Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Abinda yasa magidanci ya banka wa budurwarsa wuta ta kone kurmus a Benue

Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48
Hotunan auren dole da aka yi wa yarinya mai shekaru 13 da dattijo mai shekaru 48. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon dan sanda ya ki karbar cin hanci, yana jan kunnen direban a kan bashi da yayi

A wani labari na daban, Ali Ndume, sanata mai wakiltar kudancin Borno, ya ce da yawa daga cikin wadanda suke karkasin shugaban kasa Muhammadu Buhari barayi ne.

A ranar Lahadi, gidan talabijin din Channels sun yi hira da sanatan inda ya sanar da hakan, ya ce akwai mutanen da suke kokarin ganin bayan cigaba a mulkinsa.

Bayan an tambayeshi a kan yadda mulkin APC yake tafiya, cewa yayi gaskiya ba ya farinciki da tafiyar ta shekaru 5. Duk da suna yin iyakar kokarinsu, amma akwai gurabe da dama da ya kamata a cike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel