Obasanjo zai nufi kasar Ethiopia domin aiwatar da wani babban al'amari
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo zai nufi kasar Ethiopia
- Zai je ne don daidaita gwamnatin tarayyar kasar da TPLF, kamar yadda AFP ta ruwaito
- Amma kuma dai gwamnatin kasar Ethiopia ta nuna bata bukatar sasanci da TPLF
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, zai je kasar Ethiopia sasanci. Zai sasanta tsakanin gwamnatin kasar ne da TPLF, duk da gwamnatin ta nuna karara cewa ba ta so a taso da batun.
Kamar yadda labarin ya bayyana, shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya yi maganar a shafinsa na Twitter, amma sai ya goge.
Gwamnatin kasar ta ce, jam'iyya mai mulki a Tigray, ta ki amincewa da sasanci tsakaninta da gwamnatin tarayyar tun shekaru 2 da suka wuce.
KU KARANTA: Shugabancin kasa a 2023: PDP na fuskantar babban kalubale a kudu maso gabas
Kamar yadda ministan harkokin waje na Ethiopia, Redwan Hussain ya sanar da manema labarai a Addis Ababa, ya ce "Duk wani kokarin sasanci zai iya janyo fadace-fadace da tayar da zaune tsaye.
"Babu wata kasa da za ta zauna da bangarenta da suke ikirarin suna da kayan yaki kuma suna yunkurin kai musu hari."
Yanzu haka, tsohon shugaban kasar yana hanyarsa ta zuwa Addis Ababa don sasanci, kamar yadda kakakinsa, Kehinde Akinyemi ya yanka a cikin labaran AFP.
KU KARANTA: Ndume: Buhari na zagaye da manyan barayi a mulkinsa
A wani labari na daban, a jihar Enugu, wani mai wa'azi, Ven. Henry Ibeanusi, a ranar Lahadi ya ce Ubangiji ya samar da aure don mutum ya samu cika da farinciki.
"Hakan yana nufin duk wani namiji ba ya samun cikar kamala da farinciki, matukar ba shi da aure," cewar Ibeanusi a wani wa'azi da yayi a cocin Anglican dake jihar Enugu.
Ibeanusi ya ce, Adam shine mutumin da yafi kowa wadata a duniya a lokacinsa, yana da dabbobi, ma'adanai da wuri mai yalwa, amma bai samu farin ciki ba sai da Ubangiji ya samar masa da mata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng