Ndume: Buhari na zagaye da manyan barayi a mulkinsa

Ndume: Buhari na zagaye da manyan barayi a mulkinsa

- Buhari yana iyakar kokarinsa, mutanen da ke kasansa ne maanyan barayi, cewar Sanata Ali Ndume

- Sanatan kudancin Borno, Ali Ndume, yace ana cin amanar shugaban kasa Buhari ta karkashinsa

- Ndume ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels

Ali Ndume, sanata mai wakiltar kudancin Borno, ya ce da yawa daga cikin wadanda suke karkasin shugaban kasa Muhammadu Buhari barayi ne.

A ranar Lahadi, gidan talabijin din Channels sun yi hira da sanatan inda ya sanar da hakan, ya ce akwai mutanen da suke kokarin ganin bayan cigaba a mulkinsa.

Bayan an tambayeshi a kan yadda mulkin APC yake tafiya, cewa yayi gaskiya ba ya farinciki da tafiyar ta shekaru 5. Duk da suna yin iyakar kokarinsu, amma akwai gurabe da dama da ya kamata a cike.

A cewarsa, duk da kokarinsu, sai mutane sun zagesu, jaridar The Cable ta wallafa.

Buhari ba shi da matsala, barayi ne ke zagaye da shi, Ndume
Buhari ba shi da matsala, barayi ne ke zagaye da shi, Ndume. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Duk namijin da bashi da mata ba cikakke bane, bashi da farin ciki, Babban malami

Ya ce shugaba Buhari sai dai ya bayar da umarni, amma ba zai iya zuwa yayi ayyuka da kansa ba, don haka mafi yawan matsalolin daga masu yin ayyukan ne.

Ya bayar da misalin yadda shugaba Buhari ya amince da biyan naira biliyan 500 don samarwa mutane ayyukan yi, musamman wadanda suka gama karatu kan fannin koyarwa.

Ya ce amma idan aka ji yawan mutanen da suka amfana, za a sha mamaki. Yawanci ba a dauka ba ma.

KU KARANTA: Duk namijin da bashi da mata ba cikakke bane, bashi da farin ciki, Babban malami

A wani labari na daban, hukumar 'yan sandan jihar Bauchi, sun kama wani saurayi mai shekaru 18, bisa zargin yanka wani saurayi a kan budurwa, shafin Linda Ikeji ya wallafa hakan.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Ahmed Wakil, ya sanar da hakan a wata takarda da ya saki a kan lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng