Abinda yasa magidanci ya banka wa budurwarsa wuta ta kone kurmus a Benue

Abinda yasa magidanci ya banka wa budurwarsa wuta ta kone kurmus a Benue

- Idan baka mutu ba, baka gama ganin abubuwan ban mamaki ba

- Wani mutum a jihar Benue ya banka wa kansa da budurwarsa wuta sun kone kurmus

- Ya dauki wannan matakin ne saboda ta ki amincewa da tayin aurensa

Wani al'amari mai firgitarwa ya faru a jihar Benue, inda wani Nicodemus Nomyange, mai shekaru 40 da haihuwa, ya banka wa kansa da budurwarsa, Shinnenge Pam, wuta, a anguwar Inikpi.

The Nation ta ruwaito yadda Nomyange, wanda yake da yara kuma ya jima yana soyayya da Pam na wani lokaci, ya bukaci aurenta.

Rahotanni sun nuna yadda Pam ta watsa masa kasa a ido, inda ta ki amince da tayin aurensa, a cewarta ta gwammaci auren mutumin da bai taba aure ba.

KU KARANTA: Duk namijin da bashi da mata ba cikakke bane, bashi da farin ciki, Babban malami

Cikin fushi, a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, mutumin ya nufi gidan da take zama, ya rufe kofofi ya banka wa gidan wuta. Duk da kokarin makwabta na cetonsu, amma abin ya ci tura.

Nomyange ya rasu take a nan, ita kuma Pam ta rasu ana hanyar kai ta asibiti, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Abinda yasa magidanci ya banka wa karuwarsa wuta ta kone kurmus a Benue
Abinda yasa magidanci ya banka wa karuwarsa wuta ta kone kurmus a Benue. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Benue ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

KU KARANTA: Da duminsa: Sabbin mutum 152 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya

A wani labari na daban, Nana Aba Anamoah, ta canja rayuwar wani mai talla a kan titi, inda ta taimaka masa har ya cika burinsa na rayuwa.

Bayan haduwarsu da makonni kadan, saurayin mai suna Ebetoda ya samu cikar burinsa. A ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba, 2020, Nana ta wallafa wani bidiyo, wanda ta hadu da wasu samari 2 a titi.

Bayan samarin sun ga Nana a mota, sun biyo ta suna yi mata bambadanci, har suna rokonta ko zasuyi hoto tare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel