Bidiyon dan sanda ya ki karbar cin hanci, yana jan kunnen direban a kan bashi da yayi

Bidiyon dan sanda ya ki karbar cin hanci, yana jan kunnen direban a kan bashi da yayi

- Wani bidiyon ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani

- Bidiyon ya nuna wani dan sanda wanda ya ki amsar cin hanci a hannun direba

- Maimakon ya amsa cikin farinciki, sai ya bige da yi wa direban kaca-kaca

Bidiyon wani dan sandan kasar Ghana ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda aka ga wani dan sanda wanda direba ya bai wa rashawa ya ki amsa, kuma ya ja kunnensa a kan kada ya maimaita.

Har yanzu ba a samu sunan direban ba, amma alamu sun nuna dan yankin Volta ne, mazaunin anguwar Akan, saboda yanayin yadda yake magana a yaren Twi, da harshen Ewe.

A bidiyon, dansandan ya dakatar da wata mota mai suna 'Mahama Camboo' don ya dudduba, The Nation ta ruwaito.

Ya bukaci direban ya kawo lasisin iya tuki, kawai sai direban ya dauko kudi ya sakala a cikin takardar.

A cikin bidiyon, nan da nan fuskar dan sandan ta canja bayan ya ga kudin, sai dan sandan ya umarci direban ya tsaya gefe.

KU KARANTA: Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako

Bidiyon dan sanda ya ki karbar cin hanci, yana jan kunnen direban a kan bashi da yayi
Bidiyon dan sanda ya ki karbar cin hanci, yana jan kunnen direban a kan bashi da yayi. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

Sai ya koma wurin direban yana tambayarsa dalilin yin hakan, amma direban ya fara bashi hakuri.

"Kudinka ba za su amfane ni da komai ba, don na fika samu. Kasan nawa ake biyana?" Dan sandan ya tambayeshi cikin fushi.

Wani cikin fasinjojin motar ne ya dauki bidiyon artabun da ke faruwa tsakanin direban da dan sandan, wanda ya so a ce dan sandan ya amshi cin hancin, sai ya ga akasin hakan.

KU KARANTA: Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako

A wani labari na daban, wani al'amari mai firgitarwa ya faru a jihar Benue, inda wani Nicodemus Nomyange, mai shekaru 40 da haihuwa, ya banka wa kansa da budurwarsa, Shinnenge Pam, wuta, a anguwar Inikpi.

The Nation ta ruwaito yadda Nomyange, wanda yake da yara kuma ya jima yana soyayya da Pam na wani lokaci, ya bukaci aurenta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel