Yaro Ɗan shekara 14 ya kashe duka ahalinsu bayan gano mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce.

Yaro Ɗan shekara 14 ya kashe duka ahalinsu bayan gano mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce.

- Wani yaro mai shekaru 14 ya kashe dukkan mutanen gidansu bayan ya gano cewa ba matar babansa ce ta haife shi ba

- An gurfanar da yaron a gaban kotun yara kafin daga bisani a yanke masa hukuncin dauri a kurkukun yara

- Yaron ya hallaka mahaifinsa, matar da ta rike shi da 'ya'yan da ta haifa guda uku

Wani matashin yaro ya harbe iyayensa da ƴan'uwansa ƙanana guda 3 har lahira bayan ya gano cewa wadda ya ɗauka a mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce da ta rike shi.

Sai dai kuma duk da ya kashe 'yan uwansa yaron ko kaɗan bai nuna nadamarsa ba.

A yanzu haka yaron mai suna Masom Sisk, ya na da shekaru 15 a duniya.

Wanda ake zargi da kisan kiyashin kwata-kwata bai nuna damuwa a kan irin ɓarnar da ya aikata ba. Ana zarginsa da laifin ne a kotun yara ta Limestone County,Alabama,a watan Satumbar 2019.

Shugaban sashen wa'adin gyara hali na ɓangaren yara a Limestone County,Jami'i Tara Pressnell yace;.

"Mason bai nuna wata alamar damuwa ko nadama a bisa laifin da ake tuhumarsa na kashe iyalansa ba. Lokacin da ake tsare dashi bai taɓa hira ko magana akan iyalinsa ba ko kaɗan."

Matashin bai nuna kaico da nadamar aikita laifin da yayi ba. Ana tuhumarsa ne yi a matsayin baligi da laifin kashe rayuka biyar murus har lahira.

KARANTA: Dalilin da yasa na sace ɗalibata ƴar shekara takwas; Matashin Malami

An ce ya yi harbe-harben ne jim kaɗan bayan ya gano cewar Mary Sisk, ƴar shekara 35, ba ita ce uwar data haife shi ba, duk da har yanzu masu bincike basu tabbatar da batun ba.

Ana zargin Sisk da kashe mahaifinsa John Sisk,mai shekara 38, Kishiyar babarsa Mary Sisk, mai shekaru 35, ɗan uwansa, Grayson, mai shekaru 6, ƴar uwarsa; Aurora, mai shekaru biyar, da kuma ɗan uwansa jinjiri ɗan wata shida mai suna Colson a gidansu dake Elkmont.

Yaro Ɗan shekara 14 ya kashe duka ahalinsu bayan gano mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce.
Yaro Ɗan shekara 14 ya kashe duka ahalinsu bayan gano mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce.
Asali: UGC

Alƙalin kotun yara, mai shari'a Mathew Huggins ya ce babu wani dalili da zai nuna Sisk ya na da taɓin hankali ko matsalar ƙwaƙwalwa

lamarin mai rikitarwa gami da ɗimautarwa , a saboda haka ne kotu ta bayar da umarnin a cigaba da tsare shi a gidan yarin Limestone County.

KARANTA: Tsadar kudin dako ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki a Nigeria; Ministar Kuɗi

Rahotanni sun nuna yadda Sisk ya ke kammala aikinsa na makaranta da mu'ammala tare da sauran yara a wajen ajiye yara masu laifi na jihar Tennessee.

Da farko an yi zaton Sisk zai ɗorawa wani zargin,sai dai ya amsa da bakinsa cewa shine ya aikata ta'asar lokacin da aka tambaye shi a gaban kotu.

Kishiyar mahaifiyarsa, Mary, malama ce da ɗalibai suke ƙaunarta a makarantar Mountain Gap tare da mahaifin Sisk, mai suna John, ƙwarren mai aikin kwalliya da zanen fuska wanda ya kasance fitacce kuma mutum mai son zaman lafiya, barkwanci da raha tare da abokansa da kuma abokan aikinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel