Dalilin da yasa na sace ɗalibata ƴar shekara takwas; Matashin Malami

Dalilin da yasa na sace ɗalibata ƴar shekara takwas; Matashin Malami

- Matashin malami mai shekaru 29 ya yi garkuwa da dalibarsa mai shekaru takwas kacal

- Malamin ya kira mahaifiyar dalibar tare da neman ta biya kudin fansa naira dubu dari biyu

- Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da dabara da hikima wajen kama malamin mai suna Odugbesan Ayodele Samson

Wani malami ɗan shekara ashirin da tara ya shaidawa jami'an ƴan sanda cewa shaiɗan ne ya tunzura shi har ta kai jallin ya ƙwamushe ɗalibarsa ƴar shekara takwas a jihar Ogun.

Mutumin wanda ƴansanda suka bayyana sunansa a matsayin Odugbesan Ayodele Samson, an kama shi ne sakamon sace ɗalibarsa ƴar shekara takwas a ranar 4 ga watan Nuwamba 2020.

Mai magana da yawun ƴansandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama malamin ne bayan da mahafiyar yarinyar, Fatimat Akeeb, ta shigar da korafi a ofishin ƴansanda da ke Ajuwon.

Mahaifiyar ta sanar da cewa ɗiyarta ta je makaranta a unguwar Arifania da ke ƙaramar hukumar Akute, jihar Ogun, amma ba ta dawo gida ba har ƙarfe shida (6pm) na yammacin ranar.

KARANTA: Arewa: Akwai cin amana a tsakanin sojoji; rundunar soji ta koka

Ta faɗawa ƴansanda cewa ta samu kiran waya daga wani wanda bata san kowaye ba, ya na cewa ta biya ₦200,000 idan tana son ɗiyarta a raye.

Ta shaidawa ƴansanda cewa mai kiran nata yace wani ne ya kawo masa yarinyar kuma ba zai sake ta ba har sai an biya kuɗin."

Dalilin da yasa na sace ɗalibata ƴar shekara takwas; Matashin Malami
Odugbesan Ayodele Samson @Thenation
Asali: Twitter

A cewar rahoton DPO na ofishin ƴansandan Ajuwan, SP Andrew Akinsaye, ya umarci jami'ansa a kan su tabbatar sun gano wanda ya aikata laifin ta hanyar amfani da salo da fasaha irin na aikin ɗansanda.

Tuni kwalliya ta biya kuɗin sabulu tunda 'yan sanda sun yi ram da mai laifin har maɓoyarsa.

KARANTA: Buhari ya amince da gina sabbin cibiyoyin nazari da bincike 12 a Nigeria

"Domin kada a cutar da yarinyar, an yaudari mai laifin ta hanyar biyansa rabin kuɗin fansar da ya nema, daga nan kuma aka dinga bin diddiginsa har zuwa inda ya ɓoye yarinya aka ceto ba tare da ko ƙwarzane ba.

"A tuhumar da mukayi masa, ya amsa laifinsa, sai dai yace sharrin shaiɗan ne, a gafarce shi,".

Kwamishinan ƴansandan jihar Ogun, Edward Ajogun, ya umarci a maida binciken ƙarƙashin sashen hana garkuwa da mutane na rundunar don cigaba da tsawaita bincike da tuhuma.

Ajogun ya ja hankalin iyaye su kula da motsin ƴaƴansu daga makaranta zuwa gida don karesu daga miyagun mutane wato kura da fatar akuya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel