2023: Zan fice daga PDP zuwa APC, in ji Gwamnan Ebonyi

2023: Zan fice daga PDP zuwa APC, in ji Gwamnan Ebonyi

- Dave Umahi, gwamnan Jihar Ebonyi ya shaidawa shugabannin jam'iyyar PDP cewa zai fice daga jam'iyyar

- Jam'iyyar APC mai mulki itace inda yake shirin komawa saboda yana ganin cewa zasu bawa dan yankinsa ta kudu takara a 2023

- Amma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa a jam'iyyar ta PDP matukar zasu bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara

Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya gaya wa shugabancin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata cewa zai bar jam'iyyar.

Ya ce zai koma jam'iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APCn zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.

Umahi ya kuma bayyana cewa ya riga ya yanke shawara kuma bazai chanja ba.

Shugabannin da suka jagoranci taron sun yi kokarin gamsar da gwamnan kada ya bar jam'iyyar amma a banza.

Zan fice daga PDP zuwa APC - Gwamnan Ebonyi
Zan fice daga PDP zuwa APC - Gwamnan Ebonyi. Hoto: elombah.com
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

Baya ga Secondus, wanda suka halarci taron a gidan gwamnan Ebonyi da ke Abuja, akwai mataimakin Sakataren PDP Agbo Emmanuel, Sakataren tsare tsare Austin Akobundu, da sauran Shugabannin jam'iyya.

Gwamnan yaji dadin yadda ya karbi bakoncin shugabannin PDP amma hakan bai sa ya fasa ya janye kudirinsa ba.

Shugabannin sun gaya masa babu bukatar ya bar jam'iyyar don komawa APC.

Wata majiya ta ce, gwamnan bai gamsu ba, yana ikirarin APC din tana shirin bawa dan yankin sa takarar shugabancin kasa.

Yayi alkawarin zama a PDP matukar zasu bawa dan yankin sa takara.

KU KARANTA: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

Daya daga cikin majiyar ta ce, "ina ji ya riga ya gama zartar da hukunci. Mun fada masa babu bukatar ya bar jam'iyyar da ta kai shi matakin mataimakin gwamna, shugaban jam'iyya a jaha, gwamna har sau biyu, amma duk da haka yaki yarda.

"Yana so ne dole sai mun damka kujerar takarar shugabancin kasa ga yankin sa. Baza mu iya haka ba. Ba haka ake tafiyar da jam'iyya ba. Ya ce mana zai bar jam'iyya. Wannan ne abun da muka samu daga gareshi.

"Da aka tuntube shi, Secondus ya tabbatar da cewa shugabannin jam'iyya sun gana da Umahi.

Sai dai, bai bayyana komai dangane da taron ba, yana ikirarin taron anyi ne akan abin da ya shafi kasa.

Awani rahoton, an samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan 'yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma'aikatar JinKai da Kare Bala'i.

The Channels tv ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma'aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk gabatar ke kare kasafin kudin ma'aikatar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel