Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

- Wanda ya yi karar Rahama Sadau wurin 'yan sanda ya yi ikirarin cewa fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ne suka hana a kama ta

- Lawal Gusau, wanda ya yi karar Rahama Sadau wurin 'yan sanda ya ce bai ji dadin abinda kwamishinan ya yi ba

- Ya ce an kama kanin Rahama ana daf da kama ta kawai sai wani kwamishina ya yi waya ya ce a kyalle ta wai zata kai kanta Kaduna kuma har yanzu bata tafi ba

Wani mutum, Lawal Gusau, wanda ya shigar da kara ga Sufeto Janar na 'yan sanda, Mohammad Adamu, akan badakalar Rahama Sadau ya yi ikirarin cewa wasu manyan kusoshi a fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda suna kare jarumar kannywood din daga shiga komar hukuma

Idan za a iya tunawa Sadau dai ta wallafa hotunan tsiraici a shafukan sada zumunta, wanda hakan ya jawo kalaman batanci.

Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta
Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

Jarumar ta goge hotunan kuma ta nemi afuwar daukacin al'umma.

Sai dai wani da abin ya dama, Lawal Gusau ya shigar da kara gaban Sufeto Janar, yana rokon a kama tare da gurfanar da jarumar "saboda zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa".

Da yake shaidawa jaridar Punch ranar Talata a Kaduna, Gusau ya bayyana cewa kama Rahama Sadau ya samu tsaiko saboda wani kwamishinan 'yan sanda da ba a san kowanene ba yana kareta, duk kuwa da umarnin da Sufeto janar ya bayar.

KU KARANTA: Manyan 'yan siyasa sun hallarci ɗaurin auren ɗan Aliero da 'yar Yariman Bakura a Sokoto

A cewarsa, lokacin da kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna ya tura jami'an sa Abuja don kama Rahama, ta gudu maboya ta kuma yanki tikitin tafiya Dubai ita da iyalanta don ficewa daga kasar.

Gusau ya ce, "banji dadin yadda 'yan sanda ke tafiyar da al'amarin ba. Rahama Sadau na kokarin guduwa, ta riga ta mallaki tikitin Dubai ita da iyalanta, amma 'yan sanda sun sami nasarar kama kaninta wanda ya kaisu inda Rahama take.

"Yan sandan na gab da kama ta don kaita CID sai suka sami kiran waya daga wani kwamishinan 'yan sanda yana basu umarnin su kyale ta zata kai kanta Kaduna.

"Meye ya bawa wannan kwamishinan damar dakatar da umarnin Sufeto Janar? Yanzu, Rahama bata kawo kanta ba, ta samu kariya daga shi, da kuma wasu daga fadar shugaban kasa, wannan shine babban abin takaici."

A wani labarin, 'yan bindiga sun afka wa tawagar gwamnatin jihar Zamfara a hanyarsu ta dawowa daga Jihar Katsina.

Tawagar ta tafi Katsina ne don mika wa gwamnatin Jihar mata da yara fiye da 26 da aka ceto daga hannun masu garkuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel