Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

- Jaruma Rahama Sadau ta karyata rahotannin cewa an kama ta an kuma gurfanar da ita a gaban kuliya

- Jarumar ta ce bata san daga inda labarin ya fito ba kuma ta bukaci masu mata fatan alheri su sani cewa tana nan lafiyarta kalau ba a kama ta ba

- Rahama ta yi kira ga masu watsa labaran karyar suyi hakuri su dena don hakan ba komai zai haifar ba sai tada zaune tsaye

Rahama Sadau, fitacciyar jarumar fina finan hausa, a ranar Talata 10 ga watan Nuwamban shekarar ta karyata rahotanni da suke yawo a kafafen watsa labarai na cewa rundunar 'yan sanda ta kama ta kuma za a gurfanar da ita a kotu.

Rahama Sadau ta bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar ta Talata.

Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu
Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sanwo-Olu zai soke biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kuɗin fansho

Ta ce:

"An aiko min sakonni da dama na cewa an kama ni kuma an yanke min hukuncin zaman gidan gyaran hali a yau. Ban san daga inda wannan labaran suka fito ba. Don haka, ina kira ga mutane su dena watsa labaran karya marasa tushe.

"Ban samu gayyata daga 'yan sanda ko kotu ba. Ina son jadaddawa masu min fatan alheri cewa ina nan lafiya ta kalau kuma ba a gurfanar da ni a kotu ba. Ga wadanda ke kokarin tada zaune tsaye kan wannan batun, don Allah ku dena...!!!.

KU KARANTA: Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

"Ina cikin wani yanayi mai wahala a yanzu.

"Yanzu ba lokaci bane na yada labaran karya. Ina godiya ga wadanda suka tuntube ni, ina godiya sosai.

A wani rahoton, 'yan bindiga sun afka wa tawagar gwamnatin jihar Zamfara a hanyarsu ta dawowa daga Jihar Katsina.

Tawagar ta tafi Katsina ne don mika wa gwamnatin Jihar mata da yara fiye da 26 da aka ceto daga hannun masu garkuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel