Wani dan majalisa ya fice daga majalisa yayin da minista ke kare kasafin kudi

Wani dan majalisa ya fice daga majalisa yayin da minista ke kare kasafin kudi

- Hayaniya ta barke yayin da ministar Jinkai ke bitar kasafin kudin ma'aikatar ta shekarar 2021

- Wani dan majilisa ya zargi .yan kwamitin jin kai da yi wa minista tsawa a yayin da take gabatar da bitar kasafin kudi na 2021

- Zargin da ya janyo ficewar dan majilasar na tarayya daga dakin tattaunawar

An samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan 'yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma'aikatar JinKai da Kare Bala'i.

The Channels tv ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma'aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk ke kare kasafin kudin ma'aikatar ta.

Wani dan majalisa ya fice daga majalisa yayin da minista ke bitar kasafin kudi
Wani dan majalisa ya fice daga majalisa yayin da minista ke bitar kasafin kudi. Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta

Wasu daga cikin 'yan majalisar sun damu akan yadda aka kashewa ma'aikatar kudi, da kuma rashin gabatar da wasu takardu da minista Sadiya Umar Farouk bata yi ba.

"Bana tunanin cewa takurdun sun cika kuma sun kunshi gamsassun bayanan da ya dace da aikin mu. Yarda da wannan takardu yana nufin bamu san aikin mu ba," wani mamba a kwamitin, Awaji-Inombek Abianta, ya fada.

Daga nan kuma sai aka fara jiyo hayaniya yayin da bitar ke ci gaba da gudana, a daya bangaren kuma wani dan majalisa kuma yana zargin mambobin da dagawa minista murya wanda daga karshe ya fice daga tattaunawar.

KU KARANTA: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu

A cewarsa a maimakon a mayar da hankali a kan abinda ya dace a tambaye ta, an tsaya ana bata lokaci a kan zargin ministan da kin raba kayan abincin tallafin korona wadda daga bisani aka wawashe a dakunan ajiyan abinci.

A wani labarin da Legit.g Hausa ta wallafa, an sako Aminu Musa Abdullahi dan uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga hannun masu garkuwa.

An sace shi ne a hanyar babban birnin tarayya Abuja zuwa Kaduna a makon da ta gabata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164