Sabbin mutane 223 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 63,731

Sabbin mutane 223 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 63,731

- Maimakon samun sauki, daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa da cutar Korona

- Gwamnatin tarayya na tsoron adadin masu kamuwa da cutar zai yi tashin gwauron zabi sakamakon zanga-zangar ENDSARS

- Hukumar NCDC ta tsara shirin yadda maus bautan kasa NYSC zasu shiga sansani a fadin tarayya

Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 223 ranar Juma'a a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 63,731 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Juma'a , 6 ga watan Nuwamba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Daga cikin mutane sama da 63,000 da suka kamu, an sallami 59,844 yayinda 1154 suka rigamu gidan gaskiya.

Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu –

Lagos-85

FCT-35

Akwa Ibom-24

Enugu-18

Plateau-13

Rivers-10

Abia-7

Ebonyi-6

Anambra-5

Adamawa-4

Bauchi-3

Imo-3

Ogun-3

Oyo-3

Kwara-2

Osun-1

Taraba-1

KU KARANTA: Fastocin Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai da Bola Tinubu su na yawo a gari

Sabbin mutane 223 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 63,731
Sabbin mutane 223 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 63,731 Credit: Twitter/NCDC
Asali: Twitter

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 264

A bangare guda, Masallacin Harami a ranar Laraba ya karbi kashin farko na masu aikin Umarah daga wajen Saudiyya a mataki na uku na yunkurin dawo da ayyukan Umarah da ziyarar masallatan Harami.

A mataki na uku, masu aikin Umarah 20,000 da masallata 60,000 ake bari shiga masallacin a kowace rana a yunkurin kariya daga annobar Corona don tabbatar da lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng