Fastocin Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai da Bola Tinubu su na yawo a gari
- Fastocin wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC sun fara yawo a wurare
- Manyan APC mai mulki su na harin yadda za su gaji Buhari a zaben 2023
- Wadanda hotunan na su ke yawo sun karyata jita-jitar su na neman mulki
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa jagororin jam’iyyar APC mai mulki su na tsara yadda za su tunkari zaben shugaban kasa a 2023.
Manyan ‘yan siyasar su na harin kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari da za ta kare a 2023.
Rahotanni daga majiya mai karfi sun bayyana cewa wasu ‘ya ‘yan APC sun bude manyan ofisoshin yakin neman zabe a boye a garin Abuja.
KU KARANTA: Buhari ya sake ba 'Yan Najeriya hakuri
Kawo yanzu fastocin takarar wadannan ‘yan siyasar sun fara yawo a babban birnin tarayya Abuja.
Hotunan takarar Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai sun cika lunguna da sakoki a birnin tarayya.
Hotunan takarar Ministan da Gwamnan su na dauke da taken ‘Yau ba za ta zama yadda ake so ba, amma gobe za ta fi yau kyau; da ‘Zabin al’umma.
Kafin nan kuma an kaddamar da jirgin yakin neman zaben Bola Tinubu. Masu goyon-bayan jagoran na APC sun yi wa kansu da take da BAT 23.
KU KARANTA: An gurfanar da Matasa saboda sun yi zanga-zanga a Abuja
Wata kungiya ta Bola Tinubu da ake kira Young Professionals for Tinubu (YPT) 2023, sun ce su na da rajista a jihohin kasar nan 36 da birnin tarayya.
Rotimi Amaechi ya nuna cewa sam bai san da wannan lamari, haka zalika shi ma gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bai da masaniyar fastocin.
Yanzu haka an hurowa Shugabannin jam’iyyar APC wuta su sauka, su gudanar da sabon zabe.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng