KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka: Trump ya sha kaye 290-214

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka: Trump ya sha kaye 290-214

A yau, Talata, 13 ga Nuwamba, zaben shugaban kasan Amurka ke gudana: Yan Amurka sun fito kwansu da kwarkwatansu domin zaben shugaban da zai jagorancesu shekaru 4 masu zuwa.

Masu takara a zaben nan sune shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da Joe Biden na jam'iyyar Democratic.

Legit.ng za ta kawo muku bayanan kai tsaye kan yadda abubuwa ke gudana.

KAI TSAYE: Yadda zaben kasar Amurka ke gudana tsakanin Trump da Biden
KAI TSAYE: Yadda zaben kasar Amurka ke gudana tsakanin Trump da Biden
Asali: UGC

Tsohon abokin hamayyarn Biden da Atiku sun tayashi murya

Daga karshe, Joe Biden ya lashe zaben shugabancin kasar Amurka

Bayan kwanaki hudu ana kirgan kuri'u, tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya lshe zaben kujeran shugaban kasar Amurka.

Trump ne shugaban kasan Amurkan da ya gaza zarcewa kan kujeran cikin shekaru 30.

Joe Biden ne mutum mafi yawan shekaru da ya taba nasara a zaben shugaban kasar. Shekarun 77.

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 264
KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 264
Asali: Getty Images

Adadin jihohin da sakamako suka fito (Electoral College)

Jihohin da Biden ya lashe

1. Virginia (Biden 13)

2. Vermont (Biden 3)

3. Illinois (Biden 20)

4. Delaware (Biden 3)

5. Maryland (Biden 10)

6. Massachusetts (Biden 11)

7. Connecticut (Biden 7 )

8. New Jersey (Biden 14)

9. Rhode Island (Biden 4)

10. New York (Biden 29)

11. New Mexico (Biden 5)

12. Washington DC (Biden 3)

13. Colorado (Biden 9)

14. California (Biden 55)

15. Oregon (Biden 7)

16. New Hampshire (Biden 4)

17. Washington (Biden 12)

18. Hawaii (Biden 4)

19. Minnesota (Biden 10)

20. Maine (4)

21. Arizona (11)

22. Wisconsin (10)

23. Michigan (16)

24. Pennsylvania

25. Nevada

Jihohin da Trump ya lashe

1. Utah (Trump 6)

2. Ohio (Trump 18)

3. Iowa (Trump 6)

4. Montana (Trump 3)

5. Florida (Trump 29)

6. Texas (Trump 38)

7. Kansas (Trump 6)

8. Missouri (Trump 10)

9. Nebraska (Trump 5)

10. North Dakota (Trump 3)

11. South Dakota (Trump 3)

12. Wyoming (Trump 3)

13. Louisana (Trump 8)

14. Alabama (Trump 9)

15. Mississippi (Trump 6)

16. Oklahoma (Trump 7)

17. Tenessee (Trump 11)

18. Kentucky (Trump 8)

19. West Virginia (Trump 5)

20. South Carolina (Trump 9)

21. Arkansas (Trump 6)

22. Indiana (Trump 11)

Madogara: Aljazeera

Yanzu jihohin da ake sauraron sakamakonsu sune Georgia, North Carolina, Nevada, Michigan, da Pennsylvania.

Yayinda yake gab da nasara a zabe, Biden ya yiwa Trump raddi

Joe Biden ya lashi takobin cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, bai isa ya toshewa mutane baki ba. Ya ce sai an kammala kirgan kuri'u a dukkan jihohi kafin a ce an kammala zabe.

Biden yace: "Ba za'a toshewa mutanenmu baki ba, ba za'a hanamu magana ba kuma ba zamu sallama ba. Wajibi ne a kirga dukkan kuri'u."

Da duminsa: Joe Biden ya kwace jihar Pennsylvania hannun Trump, ya wuceshi da kuri'u 917

Dan takaran shugaban kasar Amurka karkashin jagorancin Joe Biden ya zarcewa Donald Trump a jihar Pennsylvania da kuri'u 5000, kuma har yanzu ba'a kammala kirga ba.

Da duminsa: Joe Biden ya kwace jihar Georgia hannun Trump, ya wuceshi da kuri'u 917

Dan takaran shugaban kasar Amurka karkashin jagorancin Joe Biden ya zarcewa Donald Trump a jihar Georgia da kuri'u 917, kuma haar yanzu ba'a kammala kirga ba.

Idan Biden ya samu nasara a Georgia, zai zama dan jam'iyyar Democrat daya da ya ci zaben jihar tun 1992.

Biden na gab da kamo Trump a kuri'un jihohin Georgia da Pennsylvania

Jihohi biyu da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ke sa ran ci domin samun nasara a zabe sun fara kubucewa daga hannunsa.

A jihar Pennsylvania, ranar Laraba bayan zabe Trump ya zarcewa Biden da kuri'a sama da 500,000, amma a yanzu haka, tazararr ta sauko dubu 22,389 kuma saura kuri'u sama da 100,000 da ba'a kirga ba tukun daga birnin Philadelphia kuma yawancin masoyan jam'iyyar Democrat ne.

Ga yadda sakamakon yake yanzu haka a Pennsylvania:

Trump - 3,285,239

Biden - 3,262,850

A jihar Georgia kuwa inda Trump ya zarcewa Biden da dubunnan kuri'u amma yanzu hakan tazarar ta sauko kuri'u kasa da 1500.

A cewar rahotanni, saura kuri;u 16,000 da ba'a kirga ba tukun daga birnin Atlanta kuma yawancin masoyan jam'iyyar Democrat ne.

Ga yadda sakamakon yake yanzu haka a Georgia:

Trump - 2,448,056

Biden - 2,446,577

Ga yadda sakamakon zaben gaba daya yake:

Biden - 73,534,059 | 50.46%

Trump - 69,799,702 | 47.9%

Kuma dai! Kotu ta biyu ta yi watsi da karar da Trump ya shiga a jihar Michigan

Bayan watsi da kararsa da akayi a jihar Georgia, wata kotun jihar Michigan ta kuma watsi da karar Trump inda ya bukaci a dakatad da kirgan kuri'u a jihar.

Kotu ta yi watsi da karar da Trump ya shigar, ta ce a cigaba da gashi

Wani Alkalin kotun jihar Georgia ya yi watsi da karar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar Amurka, Donald Trump. ya shigar kan kuri'un da aka kada ta akwatin sako.

Kwamitin Trump ta bukaci kotun ta tabbatar da cewa an bi dokokin jiha kan kuri'un da mutane suka kada gabanin ranar zabe ta akwatin sako.

An sake kayar da Trump a jihar Michigan

Sakamakon zaben kasar Amurka: Trump ya sake shan kaye a jihar Michigan , Biden ya samu karin makin Electoral College 16

Trump - 213

Biden - 264

Adadin jihohin da sakamako suka fito (Electoral College)

Jihohin da Biden ya lashe

1. Virginia (Biden 13)

2. Vermont (Biden 3)

3. Illinois (Biden 20)

4. Delaware (Biden 3)

5. Maryland (Biden 10)

6. Massachusetts (Biden 11)

7. Connecticut (Biden 7 )

8. New Jersey (Biden 14)

9. Rhode Island (Biden 4)

10. New York (Biden 29)

11. New Mexico (Biden 5)

12. Washington DC (Biden 3)

13. Colorado (Biden 9)

14. California (Biden 55)

15. Oregon (Biden 7)

16. New Hampshire (Biden 4)

17. Washington (Biden 12)

18. Hawaii (Biden 4)

19. Minnesota (Biden 10)

20. Maine (4)

21. Arizona (11)

22. Wisconsin (10)

23. Michigan (16)

24. Pennsylvania

25. Nevada

Jihohin da Trump ya lashe

1. Utah (Trump 6)

2. Ohio (Trump 18)

3. Iowa (Trump 6)

4. Montana (Trump 3)

5. Florida (Trump 29)

6. Texas (Trump 38)

7. Kansas (Trump 6)

8. Missouri (Trump 10)

9. Nebraska (Trump 5)

10. North Dakota (Trump 3)

11. South Dakota (Trump 3)

12. Wyoming (Trump 3)

13. Louisana (Trump 8)

14. Alabama (Trump 9)

15. Mississippi (Trump 6)

16. Oklahoma (Trump 7)

17. Tenessee (Trump 11)

18. Kentucky (Trump 8)

19. West Virginia (Trump 5)

20. South Carolina (Trump 9)

21. Arkansas (Trump 6)

22. Indiana (Trump 11)

Madogara: Aljazeera

Yanzu jihohin da ake sauraron sakamakonsu sune Georgia, North Carolina, Nevada, Michigan, da Pennsylvania.

An sake kayar da Trump a jihar Wisconsin

Sakamakon zaben kasar Amurka: Trump ya sake shan kaye a jihar Wisconsin, Biden ya samu makin Electoral College 10.

Trump - 213

Biden - 248

Trumo ya yi kuka, ya ce ana yi masa magudi

"Suna iyakan kokarinsu wajen kwashe kuri'u na 500,000 da nike da shi a Pennsylvania. Hakazalika Michigan da sauransu," Trump yace.

"Kawai kuri'un Biden ake gani a ko ina, Pennsylvania, Wisconson da Michigan. Gaskiya haka bai da kyau ga kasar mu," Trump ya kara.

"Wai shin meyasa duk lokacin da aka kirga kuri'un akwatin sako lalata min abubuwa sukeyi," Trump

,

Ta fara canza zani, Biden ya tserewa Trump a Michigan, Wisconsin da Nevada

Yayinda ake cigaba da sauraron sakamakon, Biden ya kamo abokin hamayyarsa, shugaba Donald Trump, a kuri'u a jihohin Michigan, Wisconsin da Nevada.

Har yanzu ana cigaba da kididdiga....

An yiwa Trump tattaki na musamman a Najeriya

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nuna farin cikinsa kan tattakin da aka yi masa a kudancin Najeriya.

Trump ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita inda ya ce ya godewa karamcin.

An fara kirgan kuri'u a Pensylavania

Shugaba Trump ya kada kuri'arsa

Shugaban kasar Amurka, kuma dan takara ya kada kuri'arsa. Trump ya ce yana kyautata zaton zai yi nasara.

Ban taba ganin mutane sun jeru cikin layi haka ba - 'Yar majalisa Rashida Tlaib

Yayinda hira da Al Jazeera, Rashida Tlaib, yar majalisa Musulma ta farko a Amurka ta ce bata taba ganin mutane sun tsaya a layi domin zabe irin haka ba a garinta na Michigan.

Tsohon shugaban kasa Bill Clinton da matarsa Hillary wacce Trump ya lallasa a bara sun kada kuri'unsu

Tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Clinton, da matarsa kuma tsohuwar yar takara, Hillary Clinton, sun kada kuri'arsu kuma sun zabi Joe Biden.

Bill ya rubuta a Tuwita: "Hillary da Ni kuma kada kuri'armu wa Joe Biden da Kamala Harris."

An kaddamar da kada kuri'u a birnin New York da sauran wurare

An kaddamar da kada kuri'u a birnin New York, New Jersey, Virginia, da North Carolina.

Joe Biden ya samu nasara ta farko kan Trump, yayinda Trump ta dokeshi a wani

A report by CNN indicates that Joe Biden has taken all 5 votes in Dixville Notch, a small township which is one of the first to announce results on the election day.

Rahoton CNN ya nuna cewa Joe Biden ya lashe zaben garin Dixville Notch, da kuri'u 5. Yayinda Trump ya lashe zaben Millsfield da kuri'u 16, cewar DailyMail.

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng