Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci

Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci

- Babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa ta dakatar da dan takarar sanatan Bayelsa ta yamma daga tsayawa takara a zaben sanatoci da ke gabatowa

- Ta ce shekarun Peremobowei Ebebi na takardun makarantarsa da na katin zabensa da ya gabatar wa INEC su na da banbanci, bata yarda da ingancinsu ba

- Bisa wannan dalilin ne taki yarda da ingancin takardunsa, don haka ta hana shi takara kwata-kwata

Babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa ta hana Peremobowei Ebebi, dan takarar sanata a karkashin jam'iyyar APC na Beyelsa ta yamma, takara a zaben jihar da ke gabatowa.

Daily Trust ta ruwaito yadda Alkali Jane Iyang ya yanke da wannan hukuncin a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, a kan matsalar ha'inci, wanda Richman Samuel, tsohon darektan harkokin cikin gida na gidan gwamnati da ke Yenagoa, ya gabatar a gaban kotu a kan dan takarar APC din.

Jaridar Legit.ng ta tattaro bayanai a kan yadda kotu ta tabbatar da rashin cancantar Samuel a matsayin dan takarar APC na zaben da ke tunkarowa.

KU KARANTA: IPPIS: Mun biya malamai fiye da albashinsu, sai da wasu suka maido da ragowa- Minista

Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci
Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci. Hoto daga Thenationonline.ng
Asali: UGC

Kotu ta tabbatar da rashin ingancin takardun makarantar Samuel da katin zabensa da ya gabatar ga INEC.

Inda alkalin yace shekarunsa na katin zaben da ya gabatar wa da INEC suna da bambanci da na takardun makarantarsa.

Har yanzu dan takarar bai riga ya ce komai ba, amma wani dan kungiyar kamfen dinsa ya roki kotu da tayi sassauci a kan hukuncin da ta yanke.

KU KARANTA: IGP ga 'yan sanda: Ku gaggauta komawa wuraren aikinku

A wani labari na daban, 'yan kwamiti sun ki amincewa da kasafin shuguban INEC, gidan talabijin na Channels suka nuna hakan a ranar 4 ga watan Nuwamban 2020.

A ranar Laraba ne kowa ya gabatar da kasafi ga 'yan majalisar wakilai, inda wasu 'yan kwamitinsa suka ki amincewa da kasafin da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya gabatar a kan ayyukan 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel