IGP ga 'yan sanda: Ku gaggauta komawa wuraren aikinku
- Sifeta janar na 'yan sanda, ya umarci 'yan sanda da su koma bakin aikinsu
- Ya ce kada su kuskura su bar bata-gari da 'yan ta'adda su cigaba da yin yadda suka ga dama
- Ya musanta labarin masu zanga-zangar EndSARS da aka ce 'yan sanda sun kai musu farmaki
Adamu ya yi wa 'yan sanda jawabi a hedkwatar Edo da ke GRA Benin, lokacin da yake ba wa 'yan sanda kwarin guiwa a kan konannun ofisoshin su da aka kona a jihar Edo.
IGP din wanda ya samu rakon mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, mataimakin sifeta janar na 'yan sanda, Shola David da kwamishinan 'yan sanda, Babatundu Kokumo, The Nation ta ruwaito.
A cewarsa: "Farmakin da aka kai wa 'yan sanda da ofisoshinsu an yi ne don a wulakantasu, kuma a nuna musu cewa mutane ba sa mara musu baya.
"'Yan sanda jami'ai ne na musamman saboda an horar da su musamman don taimakon al'umma.
"Shiyasa duk da harin da aka kai mu ku, kuka share su, kuma ku ka tsaya kai-da-fata wurin taimakonsu.
"Ina kara ba ku kwarin guiwa, kada ku sare, ku tabbatar kun cigaba da tabbatar da tsaro a wurare daban-daban."
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun rufe wata babbar hanya a Katsina
KU KARANTA: Malami: 'Yan daba sanye da kayan sojoji ne suka yi harbe-harbe a Lekki
A wani labari na daban, karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya ce an tura wa wasu malaman jami'an sama da asalin albashinsu, har wasu suka mayar wa da gwamnati kudinta, ChannelsTV ta ruwaito.
Ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ake tattaunawa dashi a gidan talabijin din Channels, inda yace ASUU ta lalata tsarin IPPIS, inda aka biyasu fiye da albashinsu, har wasu suka mayar da ragowa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng