An yi rikici tsakanin 'yan majalisa da shugaban INEC wurin bayanin kasafin kudi

An yi rikici tsakanin 'yan majalisa da shugaban INEC wurin bayanin kasafin kudi

- 'Yan kwamitin zabe sun kalubalanci kasafin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu a gaban majalisar dattawa

- A ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2020 ne shugaban INEC tare da tawagarsa suka gabatar da kasafin 2021

- Bayan ba wa Yakubu damar fara bayani, wani dan kwamitin INEC, Solomon Bob yayi yunkurin dakatar da shi

'Yan kwamiti sun ki amincewa da kasafin shuguban INEC, gidan talabijin na Channels suka nuna hakan a ranar 4 ga watan Nuwamban 2020.

A ranar Laraba ne kowa ya gabatar da kasafi ga 'yan majalisar wakilai, inda wasu 'yan kwamitinsa suka ki amincewa da kasafin da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya gabatar a kan ayyukan 2020.

Majalisar dattawa sun bukaci zantawar sirri tsakanin su da shugaban INEC din ba tare da tawagarsa ba, dangane da kasafin.

Bayan shugaban kwamitin, Aishatu Jibril Dukku ta bukaci Yakubu da ya bayar da bayanin kasafin 2020, sannan ya gabatar da kasafin 2021, sai dai kafin ta kai ga karasawa dan uwan aikinta, Hon. Solomon Bob daga jihar Rivers, ya katse ta, inda yace kwamitin ba su riga sun yi wata kididdiga ba ta wannan shekarar, ga shi kuma ana bukatar a gabatar da na shekara mai zuwa.

Dukku tayi ta kokarin yin bayanin cewa kullen COVID-19 ne ya lalata duk wani shirinsu, amma Bob ya ki barinta ta kai aya.

Take a nan ran Dukku ya baci, tace masa "Mai girma abokin aikina, ina bukatar kayi shiru," inda ta bukaci Yakubu ya fara jawabin.

Saboda wannan dalilin ne aka bukaci duk 'yan kwamiti su fita, a yi magana da shugaban INEC.

Bayan ya gabatar da kasafin 2020, sai Hon. Uzoma Nkem-Abonta ya kawo shawara wacce Hon Tajudeen Yusuf ya amince da ita take yanke.

KU KARANTA: IPPIS: Mun biya malamai fiye da albashinsu, sai da wasu suka maido da ragowa- Minista

An yi rikici tsakanin 'yan majalisa da shugaban INEC wurin bayanin kasafin kudi
An yi rikici tsakanin 'yan majalisa da shugaban INEC wurin bayanin kasafin kudi. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan fashi da makami sun rufe wata babbar hanya a Katsina

A wani labari na daban, Muhammad Adamu, Sifeta janar na 'yan sanda, ya ce yawancin 'yan sanda mutanen kirki ne, ba kamar yadda suka yi kaurin suna sakamakon zalunci wanda ya janyo zanga-zangar EndSARS.

Ya fadi hakan ne a ranar Talata, lokacin da ya kai ziyara jihar Legas, don duba irin barna da aika-aikar da aka yi wa ofisoshin 'yan sanda a jihar.

Adamu ya sanar da kama mutane 1,590 da aka yi a fadin Najeriya, bisa zargin kai hari sakamakon zanga-zangar EndSARS, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel