IPPIS: Mun biya malamai fiye da albashinsu, sai da wasu suka maido da ragowa- Minista
- Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya ce ASUU ce ta lalata tsarin IPPIS, sanadiyyar haka suka biya malamai fiye da albashinsu
- A cewarsa, babu wani malami da gwamnatin tarayya ta rike wa albashi, don bai ga ribar da gwamnati za ta samu idan tayi hakan ba
- Ya fadi hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels suka yi dashi, inda ya ki bayar da tabaccin lokacin da malamai za su koma makarantu
Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya ce an tura wa wasu malaman jami'an sama da asalin albashinsu, har wasu suka mayar wa da gwamnati kudinta, ChannelsTV ta ruwaito.
Ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ake tattaunawa dashi a gidan talabijin din Channels, inda yace ASUU ta lalata tsarin IPPIS, inda aka biyasu fiye da albashinsu, har wasu suka mayar da ragowa.
KU KARANTA: EndSARS: Kashe 'yan sanda babban abun Allah wadai ne - El-Rufai
"Ina ganin karya ne ace gwamnati ta ki biyan malamai na tsawon watanni 8. Sannan gwamnati ba ta yi musu adalci ba, ban ga dalilin da zai sa mutane su kawo irin wannan batun ba, saboda malaman matsayi-matsayi ne," a cewarsa.
"An tura wa wasu daga cikinsu fiye da asalin albashinsu, har wasu suna maido wa. An samu matsaloli da dama a kan wannan."
Bayan an tambayesa lokacin da malaman za su koma makaranta bai bayar da wani tabbaci ba. Sai dai ya ce babu abinda zai hana malamai komawa ayyukansu.
A cewarsa, malamai za su koma ayyukansu ko da gobe ne suka so komawa. Ya ce gwamnati ta gama yin komai yadda ya dace.
KU KARANTA: Malami: 'Yan daba sanye da kayan sojoji ne suka yi harbe-harbe a Lekki
A wani labari na daban, kungiyar malaman jami'o'i ta yi bayanin dalilin da yasa yajin aikinta na tsawon watanni uku ya kasa ci balle cinyewa, duk da jerin taron da suka dinga da gwamnatin tarayya.
Kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya, ta ce hakan ya zarce har ya koma tsoratarwa tare da hada karya ga jama'a a maimakon yin kokarin ganin karshen yajin aiki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng