Yan Najeriya 111 suka kamu da cutar COVID-19, 115 aka sallama ranar Lahadi

Yan Najeriya 111 suka kamu da cutar COVID-19, 115 aka sallama ranar Lahadi

- Duk da cewa ana tunanin cutar Korona ta shafe, har yanzu daruruwan yan Najeriya na kamuwa

- Gwamnatin tarayya na tsoron adadin masu kamuwa da cutar zai yi tashin gwauron zabi sakamakon zanga-zangar ENDSARS

- Har yanzu ana samun adadin masu warkewa daga cutar sosai

Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 111 ranar Lahadi a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Talata ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 62,964 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Lahadi , 1 ga watan Nuwamba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Daga cikin mutane sama da 62,000 da suka kamu, an sallami 58,790 yayinda 1146 suka rigamu gidan gaskiya.

Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu–

Lagos-49

FCT-30

Rivers-11

Plateau-10

Ogun-4

Kaduna-3

Oyo-3

Osun-1

KU KARANTA: Ba za mu sadaukar da rayukanmu a kan ku ba, ku kare kanku - DPO ga 'yan Najeriya

Yan Najeirya 111 suka kamu da cutar COVID-19, 115 aka sallama ranar Lahadi
Yan Najeirya 111 suka kamu da cutar COVID-19, 115 aka sallama ranar Lahadi Hoto: @NCDC
Asali: Twitter

A bangare guda, Dirakta Janar na hukumar lafiyar duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus Adhanom, ya shiga killace kansa bayan haduwa da wani tabbataccen mai cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan a shafinsa ta Tuwita @Dr.Tedros.

A cewarsa: "An gano na hadu da wani mutum mai alamun cutar COVID-19, ina cikin koshin lafiya kuma babu wasu alamu tattare dani amma zan killace kaina na tsawon kwanaki masu zuwa a gida."

"Ni da abokaina a WHO zamu cigaba da tattaunawa da abokan hulda domin ceton rayukan marasa galihu,"

KU KARANTA: Kamfanonin DisCos sun yi karin kudin wuta, ya fara aiki a Nuwamban 2020

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel