Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya killace kansa kan tsoron ya kamu da cutar Korona

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya killace kansa kan tsoron ya kamu da cutar Korona

-Kwamandan yaki da cutar Korona a duniya, Dr Tedros, ya shiga sahun masu killace kansa

- Ya hadu da wani da aka tabbatar ya kamu da cutar

- Tedroos Adhanom ya lashi takobin cigaba da yakar cutar daga cikin gidansa

Dirakta Janar na hukumar lafiyar duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus Adhanom, ya shiga killace kansa bayan haduwa da wani tabbataccen mai cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan a shafinsa ta Tuwita @Dr.Tedros.

A cewarsa: "An gano na hadu da wani mutum mai alamun cutar COVID-19, ina cikin koshin lafiya kuma babu wasu alamu tattare dani amma zan killace kaina na tsawon kwanaki masu zuwa a gida."

"Ni da abokaina a WHO zamu cigaba da tattaunawa da abokan hulda domin ceton rayukan marasa galihu,"

Ghebreyesus, wanda asalin dan kasar Habasha ne ya kasance kan gaba wajen yaki da cutar COVID-19 tun lokacin da ta bulla a duniya.

KU KARANTA:An shiga halin fargaba yayinda wata bakuwar cuta ta kashe mutane 15 a Jihar Delta

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya killace kansa kan tsoron ya kamu da cutar Korona
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya killace kansa kan tsoron ya kamu da cutar Korona
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabbin zafafan hotunan Rahama Sadau ya janyo cece-kuce

A wani labarin, Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 111 ranar Lahadi a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Talata ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 62,964 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Lahadi , 1 ga watan Nuwamba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel