Ba za mu sadaukar da rayukanmu a kan ku ba, ku kare kanku - DPO ga 'yan Najeriya

Ba za mu sadaukar da rayukanmu a kan ku ba, ku kare kanku - DPO ga 'yan Najeriya

- Jami'an tsaro sun yi wani taro don kawo karshen tashin hankali da rikici a Najeriya

- Bayan faruwar lamarin ne wani DPO ya ce ba za su bai wa wani tabbacin kula da lafiyarsa ba

- A cewarsa, yadda shagulgulan karshen shekara suka gabato, ba zai bar jami'ansa su sadaukar da rayuwarsu ba

Bayan taron da jami'an tsaro suka yi a wuraren da zanga-zangar EndSARS ta fi shafa a kudancin Najeriya, wani dan sanda wanda baiso a bayyana sunansa ba, cikin wadanda sukaje taron yace bai dace ace 'yan Najeriya sun tayar da tarzoma ba.

Dan sandan, wanda DPO ne, ya sanar da PRNigeria a wata hira, cewa kamata yayi a ce 'yan Najeriya na iyakar kokarinsu wurin kiyaye kansu daga 'yan ta'adda da bata-gari a wannan lokacin.

A cewarsa, taron da manya-manyan jami'an tsaro sun samu halartar taron, inda suka tattauna a kan rikicin zanga-zangar EndSARS, wacce ta kawo tashin hankali a wurare daban-daban a Najeriya.

Ba za mu sadaukar da rayukanmu a kan ku ba, ku kare kanku - DPO ga 'yan Najeriya
Ba za mu sadaukar da rayukanmu a kan ku ba, ku kare kanku - DPO ga 'yan Najeriya. Hoto daga Newswirengr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan adawa ke daukar nauyin 'yan daba domin lalata mulkina - Gwamnan PDP ya koka

A cewarsa, "A wadannan watannin karshen shekarar, wanda bikin kirsimeti da na sabuwar shekara ke gabatowa, bana tunanin akwai wani jami'in tsaro da zai iya ba wa wani tabbas a kan tsaro."

DPO din ya tabbatar da cewa shi ba zai bar wani daga cikin jami'an da ke kasansa ya sadaukar da rayuwarsa ba a wannan lokacin.

Ya kara da cewa: "Yanzu haka ba a kai ga gyara kayan amfaninmu da aka lalata ba, yanzu haka mutane basu riga sun farfado daga tashin hankalin da suka shiga ba wacce mutanen da ya kamata su kula da rayuwarsu ne suka jefasu. To ta yaya za mu koma ayyukanmu?"

KU KARANTA: Da duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama

A wani labari na daban, hukumar sojojin Najeriya ta ce rundunar OSS, da aka samar don kawar da ta'addanci da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda 5.

Sai dai sun rasa soja daya sakamakon bata - kashin da suka yi da 'yan ta'addan a kauyen Diskiru da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Mukaddashin kakakin rundunar, Birgediya Janar Benerd Onyeuko, ya sanar da hakan a wata takarda daya bai wa manema labarai ranar Lahadi a sansanin sojoji da ke Faskari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel