Kamfanonin DisCos sun yi karin kudin wuta, ya fara aiki a Nuwamban 2020

Kamfanonin DisCos sun yi karin kudin wuta, ya fara aiki a Nuwamban 2020

- DisCos sun tabbatar da karin farashin kudin shan wuta a Najeriya

- Wannan kari ya fara aiki ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba

- Za a ga banbamci a na’urori ko kuma idan an zo biyan kudin wata

Daily Trust ta ce kamfanonin da ke raba wutar lantarki watau DisCos sun tabbatar da karin kudin shan wuta a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, 2020.

Bayan watanni biyu ana tattauna wa tsakanin shugabannin kwadago da gwamnatin tarayya a kan canjin farashin wuta, kamfanonin DisCos sun yi kari.

A ranar 1 ga watan Satumban bana ne aka yi karin wuta, wannan ya jawo kungiyoyin kwadago su ka yi barazanar tafiya gagarumin yajin-aiki a kasar.

KU KARANTA: An yi daidai da aka kara kudin wuta, cire tallafin mai - Sanusi

Bayan tattaunawar gwamnati da NLC da TUC, an dakatar da karin a ranar 28 ga watan Satumba.

Bayan lokacin da aka dauka na dakatar da karin ya wuce, NERC ta tursasa DisCos su yi hakuri su cigaba da saida wutan a kan tsohon farashin da aka saba.

Wannan kari ya zo ne shekaru bakwai cif da aka saida wutar lantarki ga ‘yan kasuwa. Gwamnati ta saida kamfanonin ne a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2013.

Rahoton da jaridar ta fitar ya nuna cewa jama’a su na kuka da wannan lamari, har ma ana ganin kwalliyar saida wutar lantarkin ba ta biya kudin sabulu ba.

KU KARANTA: An dakatar da komawa kan sabon tsarin shan wutar lantarki

Kamfanonin DisCos sun yi karin kudin wuta, ya fara aiki a Nuwamban 2020
Ministan wuta Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Shugaban hukumar NERC, James Momoh ya ce ya bada umarni a koma amfani da sabon farashin shan wuta bayan kaddamar da shirin raba na’urorin awo.

Farfesa James Momoh ya ce DisCos za su yi rangwamen 10%-31% ga wadanda wannan kari zai shafa. Yanzu haka ana tsara yadda za a fito da wannan tsari.

Wani jami’in kamfanin wuta na Abuja ya ce masu amfani da na’urar awon wuta za su fara ganin wannan canji a jiya kafin a zo kan masu shan wuta kai-tsaye.

A makon jiya ne ku ka ji cewa majalisa ta bankado ayyuka rututu da Ministan wuta, Saleh Mamman ya ware, ya kai kauyensu a cikin kasafin kudin 2021.

Ministan ya tattara ya kai wa Kauyensa ayyukan wuta 20, ya bar sauran Jihohi a tutar babu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng