An shiga halin fargaba yayinda wata bakuwar cuta ta kashe mutane 15 a Jihar Delta
- Wata cuta da ba a san kowace iri ba ce ta kashe mutum aƙalla 15 a Jihar Delta
- An samu barkewar cutar ne a yanki biyu na jihar da suka hada da Ute-Okpu da Idumesah da ke karamar hukumar Arewa maso Gabashin Ika
- Tuni aka tura kwararru kan harkar lafiya zuwa yankunan da abin ya faru domin sanin ainahin abin da ke faruwa
Akalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon barkewar wata bakuwar cuta a garuruwan Ute Okpu da Idumesa da ke karamar hukumar Arewa maso Gabashin Ika a jihar Delta, gwamnatin jihar ta bayyana.
An tattaro cewa samfurin jikin wadanda suka kamu da ma’aikatar lafiya ta diba zai yi Karin haske wajen gano cutar da kuma sanin matakin gaba da za a dauka.
Kwamishinan lafiya na jihar Delta, Dr. Mordi Ononye wanda ya yi magana a Ote Okpu, karamar hukumar Arewa maso gabashin Ika, ya ce gwamnatin jihar ta kafa wata tawaga domin warware bakuwar cutar da ta yi sanadiyar rasa rayukan fiye da mutum 15.
Wadanda suka mutun kuma sun kasance tsakanin yan shekaru 18 da 25 a makonni biyu da suka gabata.
KU KARANTA KUMA: Sabbin zafafan hotunan Rahama Sadau ya janyo cece-kuce
A cewar Ononye: "Gwamnatin Delta ta samu bayani kan wata bakuwar cuta a Ute-Okpu da Idumesah, abin da ya sa Gwamna Ifeanyi Okowa ya umarci Ma'aikatar Lafiya da ta binciki mace-macen tare da gano musabbabinsu da kuma daƙile cutar."
Ononye ya ce Okowa ya bayar da umurnin bunkasa cibiyar lafiya a Ute-Okpu zuwa cikakken asibiti, jaridar The Nation ta ruwaito.
Ya yi kira ga al’umman garin da mazauna jihar da su kula da tsafta sosai yayinda bazara ta kunno kai ta hanyar rufe abincinsu da kyau, nome ciyayi a kewayen gidajensu.
Sannan kuma su kashe beraye da kuma ci gaba da binka’idojin kare kai daga annobar korona musamman ta hanyar wanke hannu da sabulu da ruwa.
KU KARANTA KUMA: Mun yarda mun kasa taɓuka komai wa yaran Nigeria - Ministar kuɗi
An kuma tattaro cewa ana zargin wani zazzaɓi ne ke haddasa mutuwar ko kuma wata kwayar magani.
A wani labari na daban, Rundunar sojojin Najeriya ta tura tawagar mata zalla zuwa jihar Anambra domin aikin kiyaye zaman lafiya.
Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya tabbatar da wannan ci gaban a wani wallafa da yayi a shafin Twitter, inda ya kara da cewar an turo rundunar ta musamman domin tabbatar da tsaron mazauna jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng