Sabbin zafafan hotunan Rahama Sadau ya janyo cece-kuce

Sabbin zafafan hotunan Rahama Sadau ya janyo cece-kuce

- Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta wallafa sabbin zafafan hotunanta

- A cikin hotunan an gano jarumar sanye da wata doguwar riga mai budaddiyar baya

- Sai dai wannan kwaliyya tata ta bar baya da kura domin wasu daga cikin mabiyanta sun caccake ta

Shahararriyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta saki wasu zafafan hotunanta a shafin sadarwa ta Intagram.

Jarumar ta kasance cikin ado da walwali inda ta sanya doguwar riga na gani da fada.

Sai dai a daya daga cikin hotunan da jarumar ta wallafa a shafin nata, an gano yadda aka bude bayan doguwar rigar wato ma’ana dukka bayanta ya kasance a waje.

Sabbin zafafan hotunan Rahama Sadau ya janyo cece-kuce
Sabbin zafafan hotunan Rahama Sadau ya janyo cece-kuce Hoto: rahamasadau
Asali: Instagram

Hakan ya sanya wasu daga cikin mabiya shafin nata suka nuna rashin jin dadinsu a kan wannan shiga tata, yayinda wasu kalilan suka dunga koda irin kyau da shigar tayi mata.

KU KARANTA KUMA: Mun yarda mun kasa taɓuka komai wa yaran Nigeria - Ministar kuɗi

Ga wasu daga cikin sharhin da mabiya shafin nata suka yi:

111.yusra: "Ya Allahu ikon Allah sai anyi magana kuce Allah da zuciya yake anfaniya sallam na taya ki kuka wlh tin yanzu."

official_prince_abbah: "Waike yaushe zakiyi hankaline."

_ahmerdy_: "Anya za a mutu kuwa ansha kyau."

maman_bilal1: "Allah am min tubi jawmirawo yafan. Duniyare do kam badake ummugo."

fulani_fatima: "Ina kaunar wannan karfi naki, ba za ki taba yin laifi ba a iduna."

ommyterh: "Tohm Allah ya shirye mu."

fahard_star: "Ubangiji Allah yashiryar dake."

jr_mallam: "Yar Musulmai amma gabadaya bayanta a waje hakan bai kamata ba.

KU KARANTA KUMA: Wani hazikin soja ya mutu yayin ceto mata masu shayarwa a Katsina

A wani labarin, wasu matasa da ake zaton bata gari ne a birnin Kano, sun kai mamaya shagon tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isa da ke jihar.

Bata garin sun fasa shagon nata da ke kan titin Filin Jirgin Sama daura da titin Ahmadiyya, inda suka yashe komai da ya ke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel