Allah mai iko: Miji ya rasu, matar ta bi shi bayan sa'o'i kalilan

Allah mai iko: Miji ya rasu, matar ta bi shi bayan sa'o'i kalilan

- Wani abin al'ajabi ya faru a jihar Anambra inda mutuwa ta dauki wasu mata da miji kusan a tare

- Mijin, mai suna Israel Akojede ya fara rasuwa, bayan sa'o'i kadan matar mai suna Esther ta bishi

- Sun samu shakuwa kwarai, don aurensu yayi shekaru 72, hatta sutura iri daya suke sawa

Wani abin al'ajabi ya faru a Abeokuta, jihar Ogun inda Israel Akojede ya rasu babu dadewa sai matarsa Esther ta bishi, Vanguard ta wallafa hakan.

Duk da tsofaffi ne, shekarar aurensu 72. NAN ta ruwaito yadda al'amarin ya faru a wuraren Gbonagun Obantoko da ke Abeokuta, inda aka sanar da mutuwar Akojede da misalin karfe 3 na dare a ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoba, ita kuma matar ta rasu bayan awanni kadan da samun labarin mutuwar mijin nata.

Akojede ya rasu yana da shekaru 103 a duniya, yayin da matar tasa take da shekaru 98. Yaronsu na fari, mai suna Joseph Akojede, wanda ya tabbatar da mutuwar tasu yana da shekaru 70 da haihuwa, inda yace al'amarin ya ba wa kowa mamaki duk da kowa yana tunanin hakan ya faru ne saboda tsananin soyayyar da ke tsakaninsu.

A cewarsa, "Mutuwar tazo mana a ba zata amma kuma kowa yayi ta zaton hakan zai faru. Sai dai abinda nake tunani shine tsabar son da suke yi wa junansu yasa suka bar duniya kusan a tare.

"Tun ina yaro nake ganinsu tare, babu abinda ya ke rabasu, hatta suturarsu iri daya suke sanya wa, kuma da junansu suke shawara."

KU KARANTA: Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu

Allah mai iko: Miji ya rasu, matar ta bi shi bayan sa'o'i kalilan
Allah mai iko: Miji ya rasu, matar ta bi shi bayan sa'o'i kalilan. Hoto daga Gwag.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu

A wani labari na daban, tsohon sanata Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin sun fi daraja indomie fiye da rayuwar jama'a.

Ya fadi hakan ne a matsayin martani a kan bin gida-gida da gwamnoni suka umarci jami'an tsaro don kwato kayan abincin da mutane suka sata daga ma'adanar gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel