Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati

Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati

- A wurin gwamnoni, indomie ta zama gwal, yayin da rayuwar mutane ta zama azurfa, cewar tsohon sanata Shehu Sani

- Ya wallafa hakan ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani, inda ya nuna yadda gwamnati take kaskantar da mutane

- 'Yan Najeriya da dama sun yi na'am da wallafarsa, inda suka yi ta tsokaci iri-iri da ke nuna amincewarsu da wannan maganar

Tsohon sanata Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin sun fi daraja indomie fiye da rayuwar jama'a.

Ya fadi hakan ne a matsayin martani a kan bin gida-gida da gwamnoni suka umarci jami'an tsaro don kwato kayan abincin da mutane suka sata daga ma'adanar gwamnati.

Idan ba'a manta ba, sakamakon zanga-zangar EndSARS da ta koma rikici, matasa sun balle ma'adanar gwamnati suka yi ta satar kayan abinci.

Kamar yadda wasu bidiyoyi suka bayyana, yawancin matasan, kayan abinci suka yi ta kwasa cikin kwanaki 13.

Bayan faruwar lamarin ne gwamnoni suka umarci hukuma da su bi gida-gida wurin binciko kayan.

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, ya tsoratar da 'yan jiharsa, inda yace zai sa a rushe gidan duk wanda aka kama da kayan tallafin.

A wata wallafa da Shehu Sani yayi a ranar Asabar, yace: "A wurin gwamnoni, indomie ta zama zinari, yayin da rayuwar mutane ta zama azurfa."

Bayan wannan wallafar, mutane da dama sun yi ta tsokaci, suna nuna amincewarsu da maganar sanatan. Ga wasu daga cikin tsokacin:

Wani Gbemi Nath Olorungbon cewa yayi, "Mafi yawan 'yan siyasanmu basu san darajar rayuwar mutane ba sai lokacin zabe."

TheGreatKhalid ya ce, "Gwamnatinmu za ta iya zuwa gida gida don nemo kayan tallafi amma ba za ta iya bin kananun hukumomi ba don raba kayan tallafin."

KU KARANTA: Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu

Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati
Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati. Hoto daga @TheCable
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu

A wani labari na daban, wata mata ta rasa ranta a daren Litinin yayin damben kwasar kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyar karamar hukumar Kaura dake Kagoro, Daily Trust ta wallafa haka.

Daily Trust sun bayyana yadda mamaciyar, Esther Mba, wacce take da shekaru a kalla 45 ta rasa ranta sakamakon damben dibar kayan tallafin.

Kamar yadda bayanai suka zo, bata-garin sun fara kwasar kayan abincin ne da misalin karfe 7 na daren Litinin, duk da harbe-harben jami'an tsaro da na 'yan sa kai, amma abin ya ci tura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel