Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu

Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu

- Wani tsohon manomi, mai shekaru 70 ya datse mazakutarsa, saboda iyalinsa na zarginsa da amfani da ita ta hanyar da bai dace ba

- Tsohon manomin ganyen shayin, ya yi amfani da wukar kicin ne, inda ya guntule al'aurarsa don ya fita daga zargin da iyalinsa ke yi masa

- Matarsa da yaransa, suna zarginsa da amfani da al'aurarsa wurin gamsar da matan kauyensu, da kuma kashe musu duk kudin da yake samu

Wani tsohon manomi mai shekaru 70 da haihuwa, ya yanke mazakutarsa saboda zargin da iyalinsa suke masa na lalata da matan kauyensu.

Likitoci na kokarin ceto rayuwar tsohon, wanda sana'arsa noman ganyen shayi ne a Kenya, sakamakon yanke mazakutarsa da yayi da kansa.

Mataimakin sarkin kauyensu, Sylvester Sigei ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, 26 ga watan OKtoba, ya ce tsohon yayi amfani da wukar kicin wurin datse mazakutarsa, bayan iyalinsa sun zargesa da amfani da ita wurin gamsar da matan kauyensu, musamman yadda suka ga yana kashewa zawarawa kudi, maimakon iyalinsa.

KU KARANTA: Shari'ar nadin Sarkin Zazzau, artabun da aka yi a kotu tsakanin Iyan Zazzau da sauran wadanda ake kara

Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu
Tsohon manomi ya datse mazakutarsa saboda zarginsa da gamsar da matan kauyensu. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wurin wawushe tallafin korona, dattaijuwa ta rasa ranta a Kaduna

A cewar Sigei, "Bayan matarsa da yaransa sun zargesa da kashe kudin da yake samu a gona a kan matan kauyen, ya karyata zargin, don ya tabbatar musu, sai ya yanke al'aurar tasa."

Sigei ya kara da bayyana yadda mutumin yake da fili Acre 4 na noman ganyen shayi, sannan kuma kungiyar habaka shayi ta kasar Kenya ke daukar nauyin yi masa girbi da gyaran gonar.

"A cikin zargin da iyalinsa suke masa, sun hada da amfani da kudin da yake samu wurin ginawa daya daga cikin matan da yake nema gida, duk da har yau bai ginawa nasa iyalin gida mai kyau ba," cewar Sigei.

Wata majiya daga asibiti ta ce sai da aka yi awanni 3 kafin a iya mayar da mazakutar da ya guntule wa kansa.

Likitan da yake kula da lafiyarsa, Dr Phillip Blasto, yace, "Abinda zan iya cewa shine, yanzu haka tsohon na cikin hayyacinsa."

A wani labari na daban, ana tsaka da raba kayan tallafi a ranar Litinin wasu bata-gari suka dakatar da lamarin, daganan suka kwashe kayan tas sukayi awon gaba dasu, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana labaran jihohin da suka yi ta satar kayan tallafi, sai gwamnatin jihar ta yanke shawarar raba kayan abincin kananan hukumomin da aka ajiye kayan tallafinsu a Ijebu, wadanda suka hada da karamar hukumar Ode, Sagamu da Ifo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel