Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu

Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu

- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kalubalanci 'yan jarida da su dinga fadin gaskiya ba wai neman gindin zama ba a wurin gwamnati

- Ya ce aikinsu ne bayyana gaskiya komai dacinta ga al'umma, ba wai su dinga kokarin yabo ko kuma jinjina ga gwamnati ba

- A cewarsa, lokacin da ya fara magana a kan yadda SARS suke gudanar da ayyukansu, da 'yan jarida sun yi aikinsu yadda ya dace da an cimma gaci

Gwamna Nyesom Wike ya kalubalanci 'yan jaridu su dinga yin ayyukansu yadda ya dace ba wai neman gindin zama ba a wurin gwamnati ba.

Gwamnan jihar Rivers ya sanar da hakan bayan shugabannin NGE sun kai masa ziyara a gidan gwamnati da ke Port Harcourt a ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

A takardar da hadiminsa na musamman a kan harkokin labarai, Kelvin Ebiri, ya saki, Wike ya tunatar da yadda 'yan jarida ke bayyana munanan labarai ga al'umma.

A cewarsa, "Abinda na lura da shi a kanku shine, kuna yaba mana kuma kuna jinjina mana saboda wata abota ko alaka da muke da ita da ku. Kuma ba haka ya kamata ba.

"Yakamata ku kalubalance mu- mutanen da suke rike da wata kujera- don mu yi abubuwan da suka dace a lokutan da suka dace. Idan muka ga haka, za mu yi abubuwan da suka dace.

"Ina so in ba ku kwarin guiwa a kan bayyana gaskiyar abubuwan da ke faruwa a Najeriya.

"Akwai lokacin da kuke bayyana munanan abubuwan da ke faruwa a kasar nan. Idan banda ku, babu yadda mutane za su san meke faruwa. Ya kamata ku dage wurin yin ayyukanku, kuma ku bude baki kuyi magana."

Yayin da yake magana akan zanga-zangar EndSARS, ya ce;

"A lokacin da na nuna takaici na a kan yadda SARS suke gudanar da ayyukansu, da kun dasa daga inda na tsaya, kila da yanzu an kai ga gaci.

"Yanzu ku kalli yadda abubuwa suka kazanta. Matasa sun yi zanga-zangar EndSARS, kila kawai zanga-zangar suka yi amma babu shugaba.

"Har yanzu, babu wani mai hankalin da zai gane yadda suka yi hakan, sannan ba a san wanene ya shirya musu hakan ba. Idan ba'a aiki da hankali da fasaha ta ina Najeriya zata kawo karshen Boko Haram?"

KU KARANTA: Cire kudi da nayi a asusun bankinka babu izininka hakkina ne - Budurwa ga saurayi

Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu
Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za mu rushe gidajenku ko mu kwace takardunsu - Gwamna Fintiri ga masu satar tallafi

A wani labari na daban, sace-sace da matasa ke ta yi sun cigaba da faruwa a ma'ajiyar gwamnati, inda suke sace kayan tallafin COVID-19 wadanda ya kamata a raba tun lokacin da gwamnati ta saka kulle.

Duba da faruwar wannan lamarin ne 'yan sanda suka zura idanu suna kallo ana sata basu daukar wani mataki a kai, Daily Trust.

Wani 'Dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa ya yi magana a kan zura idon da 'yan sandan suka yi a kan al'amarin a matsayinsa na jami'in tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng