Buhari ya aike sakon ta’aziyya ga Ahmed Gumel ta mutuwar matarsa

Buhari ya aike sakon ta’aziyya ga Ahmed Gumel ta mutuwar matarsa

- Allah ya yi wa uwargidar shugaban kungiyar wasanni ta Olympics a Najeriya, Injiniya Habu Ahmed Gumel rasuwa

- Hajiya Ladi Gumel ta rasu tana da shekaru 56 bayan ta yi yar gajeriyar jinya

- Shugaban kasa Muhammau Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa a kan wannan rashi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga Shugaban kungiyar wasanni ta Olympics a Najeriya, Injiniya Habu Ahmed Gumel, a kan mutuwar matarsa, Hajiya Ladi Gumel.

Buhari a cikin wani jawabi daga mai ba shi shawara a kafofin watsa labar, Mallam Garba Shehu, a yau Laraba, ya kuma mika sakon jaje ga iyalai da makusantan marigayiyar.

KU KARANTA KUMA: Tallafin COVID-19: Mun raba wa gwamnoni ton 70,000 na kayan abinci - Ministar jin ƙai

Buhari ya aike sakon ta’aziyya ga Ahmed Gumel ta mutuwar matarsa
Buhari ya aike sakon ta’aziyya ga Ahmed Gumel ta mutuwar matarsa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Ya kuma yi kira garesu a kan su dauki dangana tare da koyi da kyawawan dabi’un marigayiyar sannan su yi alfahari da shaidar rayuwa ta gari da ta samu wajen kyautata kusancinta da Mahallicinta, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Shugaban kasar ya yi addu’ar neman Allah ya jikanta da Rahama tare da bai wa iyalanta juriya ta rashin da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa

Hajiya Gumel mai shekaru 56 ta mutu ta bar ’ya’ya hudu bayan ta yi fama da rashin lafiya takaitacciya.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, ya mika ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Lagas a mulkin soja kuma jigon APC, Birgediya Janar Buba Marwa, kan mutuwar kaninsa, Idris.

Buhari ya aika ta’aziyyar ne a cikin wata sanarwa da babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina, ya saki.

Alhaji Idris Marwa, wanda ya kasance babban dan kasuwa a Kaduna ya rasu a ranar Talata, bayan yar gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 57 a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel