Arziƙi a gidanmu: Buhari ya shirya wa shuwagabannin ƙasashen Senegal da Guinea Bissau liyafa

Arziƙi a gidanmu: Buhari ya shirya wa shuwagabannin ƙasashen Senegal da Guinea Bissau liyafa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gayyaci shuwagabannin ƙasashen Senegal da Guinea Bissau liyafar cin abinci

- Buhari ya shirya masu liyafar ne a yau Alhamis, 15 ga watan Oktoba, a fadarsa da ke Abuja

- Shugabannin biyu na yankin Yammacin Afrika sun zo Najeriya ne kan ziyarar aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, gayyaci Shugaban kasar Senegal, Macky Sall da takwaransa na kasar Guinea Bissau, Umaro Embalo zuwa wajen liyafar cin abincin dare a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya tattaro cewa shugabannin yankin na Yammacin Afrika biyu sun kasance a Abuja bisa ziyarar aiki lokacin da Shugaban Najeriyan ya gayyace su taron cin abincin.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yi fatali da rokon Onnoghen na tursasa Gwamnati ta biya sa N130m

Arziƙi a gidanmu: Buhari ya shirya wa shuwagabannin ƙasashen Senegal da Guinea Bissau liyafa
Arziƙi a gidanmu: Buhari ya shirya wa shuwagabannin ƙasashen Senegal da Guinea Bissau liyafa Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

An tattaro cewa Shugaban ma’aikatan Shugaban kasar, Farfesa Ibrahim Gambari da wasu daga cikin mambobin majalisa da hadiman Shugaban kasar ma sun halarci taron.

Shugaba Buhari a ranar 21 ga watan Satumba, ya yi taro makamancin wannan tare da Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo.

KU KARANTA KUMA: 'Yar majalisar jihar Ondo da aka kora don zargin zagon kasa ta yi martani

Ga bidiyon ziyarar nasu wanda fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter:

A gefe guda, mun ji cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, wanda yakai masa ziyara domin gabatar masa da rahoto a kan rikicin kasar Mali.

Kazalika, Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohin; uku na jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na jihar Jigawa, Badaru Abubakar, da na jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Ya zuwa yanzu babu wani jawabi da fadar shugaban kasa ko gwamnonin suka fitar dangane da dalilin ganawarsu da Buhari.

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa a ranar Talata, Buhari ya fara shirin ruguza hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu da suka hada da EFCC da kuma ICPC.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisar, mai taken: "Dokar hukumar gurbattun kudade".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel