Hon. Onuoha ta kawo kudirin da zai bada damar amfani da wiwi wajen bincike

Hon. Onuoha ta kawo kudirin da zai bada damar amfani da wiwi wajen bincike

- An kai kudirin neman halasta amfani da wiwi a gaban Majalisar Wakilai

- ‘Yar Majalisar Imo, Princess Miriam Onuoha, ta gabatar da wannan kudiri

- Idan har an yi na’am da hakan, za a halattawa masu bincike amfani da wiwi

Kudirin da ke neman halasta amfani da ganyen tabar wiwi wajen binciken lafiya da nazarin kimiyya ya na gaban ‘yan majalisar wakilan tarayya.

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa Honarabul Princess Miriam Onuoha mai wakiltar yankin Okigwe ta Arewa ce ta kai wannan kudiri majalisar.

A halin yanzu wannan kudiri da Hon. Miriam Onuoha ta gabatar, ya kai matakin sauraro na biyu.

Wani masanin harkar shari’a, Dr. Tonye Jaja Clinton ya bayyana wannan a wajen wani taro da kungiyar Grow Cann Africa ta shirya da ‘yan jarida.

KU KARANTA: Wani ya ba Kungiyar Izala N500m a boye domin ginin Jami’ar addini

Da ya ke magana a garin Abuja, Tonye Jaja Clinton ya bayyana irin amfanin noma ganyen wiwi da kuma fa’idar mansa da ake amfani da shi, Cannabidiol.

Grow CANN Africa ta na kokarin ganin Najeriya ta yi amfani da baiwar da Ubangiji ya yi mata na wiwi, wanda zai iya jawo mata Dala biliyan 10 a 2020.

Shugabar wannan kungiya, Uju Adaku, ta yi bayanin yadda za a iya samun riba idan aka ba mutanen kasar waje damar noman wiwi da kuma aiki da shi.

A dalilin haka ne wannan kungiya ta zauna da Jakadun kasashen Kanada da ke Najeriya da hukumomi irinsu NAFDAC, NDLEA da ma’aikatar noma.

KU KARANTA: Hadari ya barke, mota ta karya kafar wani ango a tsakiyar bikin aurensa

Hon. Onuoha ta kawo kudirin da zai bada damar amfani da wiwi wajen bincike
Princess Miriam Onuoha Hoto: LInda Ikeji
Asali: UGC

Adaku ta ce Grow CANN Africa ta na neman a rika cin moriyar wiwi a Najeriya ta hanyar kwarai. Doka ta haramta aiki da wiwi saboda bugar wa da ya ke yi.

Jaja ya bayyana cewa idan wannan kudiri ya samu karbuwa a majalisar wakilai, zai je gaban Sanatoci, daga nan kuma a mika sa zuwa teburin shugaban kasa.

A makon jiya kun ji cewa Jami'an hukumar NDLEA da ke yaki da fataucin kwayoyi, sun gano wata babbar gonar tabar wiwi a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya.

Dakarun NDLEA sun lalata wannan gonar tabar wiwi wanda darajarta ya kai akalla N1.2bn.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel