Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Malaman Jami’a su kama sana’ar noma

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Malaman Jami’a su kama sana’ar noma

- Gwamnati ta fadawa Malaman Jami’a dole sai ta IPPIS za ta biya su albashi

- Malaman Jami’a su na yajin aiki a Najeriya a kan wannan tsari da aka kawo

- Ministan ilmi ya ce gwamnati ba ta rike ASUU ba, za su iya ajiye aikin na su

Karamin ministan ilmin Najeriya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, ya yi kira ga ‘yan kungiyar ASUU na malaman jami’a, su shiga harkar noma.

Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana cewa ana bukatar karin manoma, don haka malaman makarantar na iya rabuwa da aji, su koma gona.

Ministan ilmin ya kuma yi bayani game da shirin da gwamnati ta ke yi na bude makarantu, ya ce za a rika yin darusa da rana da nufin rage cunkoso.

Nwajiuba ya bayyana haka ne lokacin da aka gayyace shi a gidan talabijin na Arise News a Abuja.

KU KARANTA: Ba da gaske Gwamnati ta ke yi ta kawo karshen yajinmu ba - ASUU

A game da dogon yajin-aikin kungiyar ASUU, ministan ya ce dama can ba saboda annobar COVID-19, malamai su ka rufe jami’o’in Najeriya ba.

Don haka ya bada shawara ga malaman jami’o’in kasar da su yi tunanin komawa noma saboda gwamnati ta na bukatar karin manoma a halin yanzu.

Mai girma Ministan ya ke cewa ASUU ta na da damar da za ta mikawa gwamnati kokon bararta, amma ya ce an biya malamai albashi har zuwa Yuli.

“Ba mu fara yajin-aiki da ASUU a kan COVID-19 ba. Dama can ASUU ta na yajin-aiki kafin zuwan annobar COVID-19." Inji Karamin Ministan tarayyar.

KU KARANTA: Ma’aikatan Jami’a sun garzaya yajin-aiki ana shirin bude Makarantu

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Malaman Jami’a su kama sana’ar noma
Jagororin ASUU a wani zama Hoto: This Day
Asali: UGC

Nwajiuba ya ke cewa daf da za a rufe makarantu, (ASUU) su ka tattara su ka tafi yajin aiki.

Ministan ya ce: “Gwamnati ba ta tsare kowa ba. Cewa ta yi idan zan biya ku, dole ya zama ta tsarin IPPIS. Za ka iya barin aikin, ka tafi ka ce ba za ka yi ba."

Ministan ya cigaba da karin bayani, ya na cewa: “Ba na son in koyar. Za ka iya samun wani abin yi. Abin da mu ke bukata a yanzu sosai su ne manoma.”

A makon nan ne kuma aka ji cewa kungiyoyin NASU da SSANU sun yi kira ga mutanensu su shiga yajin aikin mako biyu domin su ja-kunnen gwamnati.

Ma’aikatan Jami’an su na kuka da IPPIS, sun kuma ce an hana su wasu alawus da hakkokinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel