Wiz Kid ya ce Buhari ya ji da kashe-kashen da ake yi a gida ba lafiyar Trump ba

Wiz Kid ya ce Buhari ya ji da kashe-kashen da ake yi a gida ba lafiyar Trump ba

- Ayodeji Ibrahim Balogun ya fito ya caccaki Shugaban Najeriya a kan Twitter

- Mawakin da aka fi sani da Wiz Kid ya koka da yadda SARS su ke kisan gilla

- Wiz Kid ya bukaci Buhari ya ji da wannan, ya rabu da harkar kasar Amurka

Tauraron Mawaki, Wizkid Ayo, ya yi martani game da sakon da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa Donald Trump da kuma iyalinsa.

Ayodeji Ibrahim Balogun wanda aka fi sani da Wiz Kid ya yi kaca-kaca da shugaban kasarsa, ya ce ya fita harkar shugaban Amurkan, ya ji da Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan jama’a sun fito kafafen sadarwa na zamani su na kiran gwamnatin tarayya ta yi wani abu game da ta’adin Dakarun SARS.

KU KARANTA: IGP ya hana SARS tsaida Jama'a da nufin su bincike su a hanya

Mawaka irinsu Wiz Kid, Davido, Don Jazzy su na cikin wadanda su ka huro wuta a kan a kawo karshen kisan gillar da SARS su ke yi wa Bayin Allah.

A dalilin haka ne Tauraron ya yi wa shugaba Buhari raddi kan maganar da ya yi a Twitter, ya ce ya kyale Donald Trump, ya yi maganin jami’an SARS.

Ya rubuta a shafinsa: “Donald Trump ba matsalar ka ba ce! Dattijo! ‘Yan Sanda/SARS su na kashe matasan Najeriya kullum-yaumin. Ka yi wani abu”

Mawakin ya kara da cewa: “Babu abin da ya had aka da Amurka. Ka ji da kasarka!”

KU KARANTA: Hisbah ta na yi wa Matasa askin dole a Kano

Wiz Kid ya ce Buhari ya ji da kashe-kashen da ake yi a gida ba lafiyar Trump ba
Wiz Kid Ayo Hoto: BBC
Asali: UGC

Sama da mutane 60, 000 su ka yada wannan magana da WizKid ya yi a Twitter, sannan fiye da mutane 120, 000 su ka nuna maganar ta burge su a sa'a 12.

Bayan haka Tauraron mai mabiya miliyan bakwai a shafin Twitter, ya yi irin wannan kira ga gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya takawa jami’an burki.

Za ku tuna, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na cikin wadanda su ka yi maza su ka yi magana bayan jin cewa Donald Trump ya kamu da COVID-19.

Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya, yajantawa Trump da mai dakinsa Melania.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel