Ka daina zagin gwamnoninmu – PDP ta yi kakkausar gargadi ga shugaban rikon kwarya na APC

Ka daina zagin gwamnoninmu – PDP ta yi kakkausar gargadi ga shugaban rikon kwarya na APC

- Jam’ iyyar PDP ta yi gargadi da kakkausar murya ga shugaban rikon kwarya na jam’ iyyar APC

- PDP a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, ta gargadi gwamnan jihar Yobe da ya daina zagin gwamnoninta

- A cewar PDP, gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwarta sun fi na APC tabuka abun kirki

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gargadi gwamnan jihar Yobe kuma Shugaban rikon kwarya na jam’ iyyar All Progressives Congress (APC), Mai Mala Buni da ya daina zagin gwamnoninta.

Babbar jam’iyyar adawar a wasu jerin wallafa da ta yi a shafinta na Twitter a ranar 4 ga watan Oktoba, ta gargadi gwamnan da ya daina aiko wasu mutane a APC.

Domin su zagi gwamnoni da sauran shugabanninsu don kawai su janye hankalin mutane daga gazawa da matsalolin jam’iyyar mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: IGP Adamu ya haramta wa jami'an SARS wasu jerin ayyuka

Ka daina zagin gwamnoninmu – PDP ta yi kakkausar gargadi ga shugaban rikon kwarya na APC
Ka daina zagin gwamnoninmu – PDP ta yi kakkausar gargadi ga shugaban rikon kwarya na APC Hoto: @vanguardngrnews
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa jam’iyyar adawar ta yi kira ga Buni da ya tsara hanyar da ta fi dacewa domin magance gazawar APC a matakan jiha da tarayya.

Ta ce mafita zai nema maimakon kokarin amfani da wasu mutane da ba a san da zamansu ba wajen cin zarafin gwamnoni masu kokari.

PDP ta ci gaba da cewa gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwarta sun fi kokari ta kowani fannin, fiye da takwarorinsu na APC.

KU KARANTA KUMA: Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa

A gefe guda, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani a kan yawan rikici da ake ta samu yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan Ondo.

Babbar jam’iyyar adawar ta yi ikirarin cewa jam’iyyar APC na aiki tare da Gwamna Rotimi Akeredolu domin razana dan takararta, Jegede Eyitayo da mutanen jihar.

PDP ta shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daidaita gwamnan na Ondo sannan ya yi amfani da irin dabarun da ya yi amfani da su a Edo don tabbatar da zaben lumana a Ondo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel