UEFA za ta zabi ‘Dan wasan bana tsakanin Neuer, Lewandowski da De Bruyne
- Cristiano Ronaldo ya gaza shiga cikin gwarzan ‘Yan kwallon Turan bana
- Haka zalika Takawaransa Lionel Messi na Barcelona bai samu shiga ba
- Manuel Neuer, Robert Lewandoski da De Bruyne su ne su ke tashe yanzu
Hukumar kwallon kafa ta Turai watau UEFA ta fitar da sunayen ‘yan wasa uku na karshe wadanda a cikinsu za a fitar da gwarzon shekarar 2019/20.
A wannan shekara babu sunan ko daya daga cikin manyan ‘yan wasan Duniya da su ka saba fice a ko yaushe, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.
Ga yadda zabin da aka yi ya kasance:
KU KARANTA: ‘Dan wasan gaban Real ya huro wuta sai ya tashi daga kulob
1. Kevin De Bruyne (Manchester City)
‘Dan wasan tsakiyan Manchester City ya yi abin a yaba a kakar bara bayan da ya yi sanadiyyar bada kwallae 20, sannan kuma ya jefa kwallaye 13 da kansa a raga a gasar Firimiya.
2. Robert Lewandowski (Bayern)
Robert Lewandoski mai bugawa gaban Bayern Munchen shi ne ‘dan wasa na biyu a jerin. ‘Dan wasan na kasar Poland ya ci kwallaye 55, sannan ya lashe gasar gida da kuma na Nahiya.
3. Manuel Neuer
Bajintar Manuel Neuer mai tsaron gidan Bayern Munich ta sake fito da shi a shekarar bana. ‘Dan wasan da ke tsaron raga ya shafe wasanni shida ba tare da an zura masa kwallo a Turai ba.
KU KARANTA: ‘Yan wasan kwallon kafa da su ka fi yawan kwallayen kasa
Ragowar ‘yan wasan da su ke cikin sahun goma na farko su ne:
4. Lionel Messi (Barcelona)
5. Neymar Jr. (Paris Saint-Germain)
6. Thomas Müller (Bayern)
7. Kylian Mbappé (Paris Saint-Germain)
8. Thiago Alcántara (Bayern)
9. Joshua Kimmich (Bayern)
10. Cristiano Ronaldo (Juventus)
Kungiyoyin Bayern da PSG ne su ka fi kowa tarin wakilai a shekarar nan. Kungiyoyin biyu su na da ‘yan wasa bakwai. Barcelona, Juventus da Manchester City duk su na da guda.
A makon da ya gabata kun ji cewa Liverpool ta saye 'Dan wasan tsakiyan kasar Sifen, Thiago Alcántara daga Bayern Munich baya ya lashe gasar cin kofin Nahiyar Turai.
Thiago Alcantara ya na cikin 'yan wasan da su ka shiga cikin wannan jeri da aka fitar dazu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng