Mayakan Boko Haram sun kashe kwamandan rundunar soji a harin kwanton bauna

Mayakan Boko Haram sun kashe kwamandan rundunar soji a harin kwanton bauna

- Har yanzu mayakan kungiyar Boko Haram na kai hari jifa - jifa a kan rundunar sojoji a jihar Borno

- Gwamnatin Najeriya ta shafe fiye da shekaru 10 ta na yaki da kungiyar Boko Haram mai ikirarin yakin Jihadi

- Rundunar soji ta yi asarar manya da kananan dakarunta yayin yaki da mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno da sauran jihohin arewa maso gabas

Rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Ado Isa, kakakin rundunar atisayen Lafiya Dole, ya ce Kanal Bako ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa tawagarsa harin kwanton bauna yayin da suka fita sintiri.

A cikin jawabin da Isa ya fitar ranar Litinin, ya ce Kanal Bako ya rasu a asibiti duk da ya fara nuna alamun farfadowa bayan harin 'yan ta'addar.

Sai dai, Isa bai yi karin bayani a kan adadin sauran dakarun soji da su ka samu raunuka yayin harin kwanton baunar da aka kaiwa tawagar sojojin ba.

DUBA WANNAN: Ku godewa Allah: Kamata ya yi a sayar da litar man fetur N181 ba N161 ba - FG

"Rundunar atisayen Lafiya Dole ta rasa jarumi, daya daga gwarazanta na yaki, Kanal DC Bako.

"A matsayinsa na kwamanda, kullum shine a gaba idan rundunarsa za ta fita aiki.

Mayakan Boko Haram sun kashe kwamandan rundunar soji a harin kwanton bauna
Marigayi Kanal Bako
Asali: Twitter

"Da irin wannan salon jarumta ne ya jagoranci rundunarsa zuwa yankin Sabon Gari - Wajiroko a Damboa domin kawar da sauran mayakan kungiyar Boko Haram a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba.

"Dakarun soji, a karkashin jagorancinsa, sun samu nasarar dakile harin kwanton baunar da aka kai mu su tare da samun nasarar kwace makaman 'yan ta'adda.

DUBA WANNAN: Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka

"Sai dai, abin takaicin shine Kanal Bako ya samu munanan raunuka kasancewar shine a gaba yayin da sojoji ke yin musayar wuta da 'yan ta'addar da suka kai musu harin kwanton bauna da misalin karfe 10:00 na safe.

"Kanal Bako ya fara farfadowa a asibiti bayan an yi masa tiyata, har ya samu damar yin Sallah da safiyar yau, Litinin, kafin ya rasu a asibiti.

"Mu na addu'a Allah ya ji kansa," a cewar sanarwar da Isa ya fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel