Na san yadda APC, PDP, da sauransu suke zabar shugabanninsu na kasa, in ji Yari

Na san yadda APC, PDP, da sauransu suke zabar shugabanninsu na kasa, in ji Yari

- Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana cewa yana shirin neman takarar shugabancin jam’iyyar APC

- Yari ya bayyana cewa ya san komai game da yadda ake zabar shugabanni na kasa a fadin jam’iyyun siyasa

- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa tsaf zai yi aiki a matsayin shugaban APC idan aka bashi damar yin hakan

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya nuna ra’ayinsa na son zama shugaban jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa na gaba.

Tsohon gwamnan na Zamfara ya bayyana cewa idan har aka bashi damar shugabantar jam’iyyar mai mulki, toh da zuciya daya zai karbe shi.

Yari ya bayyana cewa tarin iliminsa kan yadda ake zabar shugabanni a fadin jam’iyyun kasar ne ya bashi karfin gwiwa a kan kudirinsa na son jan ragamar harkokin APC.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: An dakatar da shugaban jam'iyyar APC

Na san yadda APC, PDP, da sauransu suke zabar shugabanninsu na kasa, in ji Yari
Na san yadda APC, PDP, da sauransu suke zabar shugabanninsu na kasa, in ji Yari Hoto: zebranewsonline.com
Source: Depositphotos

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan ya ce: “Na fadi a lokuta da dama cewa na san yadda ake zabar shugaba. Imma a PDP, ANPP, CPC, na san yadda ake zabar shugaba.”

Yari ya bayyana cewa abun da ake bukata shine cewa jam’iyyun siyasa “su zauna su yi tunani sosai kan wani yanki ne zai samar da shugaba, wani yanki ne zai samar da sakatare, wani yanki ne zai samar da mataimaki.”

A baya mun ji cewa, AbdulAziz Abubakar Yari, ya bayyana cewa mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar sun shirya yin sulhun gaske yanzu bayan rikicin cikin gida tsakaninsa da Sanata Kabiru Marafa.

Bangaren Kabiru Marafa da na Yari sun kasance cikin bakin kiyayya tun gabanin zaben 2019.

Yari ya jagoranci tawagar mambobin jam'iyyar zuwa wajen shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, a Sakatariyar jam'iyyar dake Abuja.

Ya bayyana dalilan da ya sa ake bukatar sulhu a jihar, kuma ya ce dukkan abokan hamayya su gabato da niyya mai kyau.

KU KARANTA KUMA: Jihar Bauchi: Wani babban jigo a PDP ya koma APC, ya bi sahun Dogara

Amma Yari yace matsalan shine wasu daga cikin mabiya Sanata Kabiru Marafa tuni sun hada kai da gwamnatin Bello Matawalle na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel