Yanzu Yanzu: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari (ga batutuwa uku da suka tattauna a kai)

Yanzu Yanzu: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari (ga batutuwa uku da suka tattauna a kai)

- Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya a ranar Talata ya zanta da Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Hirar da suka yi ta wayar tarho ya fi karkata ga yadda za a karfafa alaka tsakanin kasashen biyu masu arzikin man fetur

- Buhari da Sarki Abdulaziz sun tattauna yaddda za a daidaita kasuwar mai ta duniya a tsakanin mambobin OPEC

Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, sarkin kasar Saudiyya a ranar Talata, 18 ga watan Agusta, ya yi hira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wayar tarho.

Hirar tasu, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya, ya karkata ne ga yadda za a daidaita kasuwar mai ta duniya.

Legit.ng ta tattaro cewa daga cikin abubuwan da suka tattauna sune muhimmancin bin dokokin yarjejeniyar kungiyar kasashe masu fitar da man fetur (OPEC) da kuma tsarin diyar da aka amince dashi daga dukkanin kasashen da ke a matsayin mambobin ta.

Yanzu Yanzu: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari (ga batutuwa uku da suka tattauna a kai)
Yanzu Yanzu: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari Hakkin mallaka: Saudi Press Agency
Asali: UGC

Shugabannin biyu sun kuma tattauna yadda za a karfafa alaka tsakanin kasashen biyu da kuma damammaki domin kara ci gabansu.

Hira tsakanin Shugaba Buhari da Sarkin Saudiyya na zuwa ne kasa da watanni uku bayan Shugaban Najeriya da Firai ministan jumhuriyyar Islama ta Fakistan, mai girma Imran Khan, sun yi hira ta wayar tarho.

Wani jawabin twitter daga shafin fadar Shugaban kasa ya tabbatar da lamarin tattaunawar tsakanin shugabannin biyu a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu.

Kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar, ganawar shugabannin biyu ta gudane na kan yadda za'a bullo da shirin rage nauyin bashi don taimakawa kasashe masu tasowa.

Har ila yau a baya mun ji cewa an samu nasarar yi wa Sarki Salman tiyata a mafitsara a babban asibitin Sarki Faisal da ke birnin Riyadh.

Sarki Salman wanda shi ne shugaban masu kula da Masallatan Harami biyu da ke Kasar Saudiya, ya nuna godiyarsa ga duk wadanda suka kira ko aiko masa da sakon fatan alheri.

Babu shakka shugabannin kasashen duniya da dama sun rika aike wa da Sarkin sako na fatan samun waraka cikin gaggawa, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Wannan sako yana kunshe cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya sanya wa hannu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng